Na gana da Buhari a Landan, zai dawo, kuma za’a sha mamaki idan ya dawo – Shugaban kungiyar matasan Arewa, Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu

Na gana da Buhari a Landan, zai dawo, kuma za’a sha mamaki idan ya dawo – Shugaban kungiyar matasan Arewa, Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu

Yayinda cece-kuce ya yawaita kan abubuwan da ke tattare da rashin lafiyan shugaba Buhari, shugaban kungiyar matasan Arewan na kasa, Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu, ya gargadi yarbawa akan kaidin da suke shiryawa.

Gujungu yace, Arewa musamman matasan Arewa na sane da kaidin da yan yankin kudu amso yamma na tuge shugaba Buhari ta hanyar amfani da rashin lafiyanshi a matsayin hujja.

Ya bayyana cewa shugabancin kungiyar ta ziyarci shugaba Buhari a Landan inda sukace yana samun sauki kuma ba da dadewa ba zai dawo gida.

Yayinda yake magana da manema labarai a ranan Juma’a. Gambo yace Yarabawa na amfani da gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, da Femi Fani Kayode wajen cimma burinsu kuma su sani cewa Arewa ba zata amince da duk wani yunkurin dauke shugabanci daga Arewa a yanzu ko 2019 ba.

Na gana da Buhari a Landan, zai dawo, kuma za’a sha mamaki idan ya dawo – Shugaban kungiyar matasan Arewa, Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu

Na gana da Buhari a Landan, zai dawo, kuma za’a sha mamaki idan ya dawo – Shugaban kungiyar matasan Arewa, Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu

Yace: “ Wadannan yan kudu maso yamman na tunanin bamu gane siyasansu bane, mun gane su kuma zamu basu mamaki idan muka shirya. Suna amfani da gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon ministan sufurin jirgin sama, Femi Fani Kayode wajen cinno ma arewa wuta da kuma shugaban kasa musamman.

" Bari in bayyana muku cewa bayan ganawarmu a nan Kaduna, mun tura wakilai Landan. Ni na jagorancin wannan tawaga saboda muna son sanin sahihin halin da ake ciki. Mun gana da shugaban kasa kuma ya fada mana wasu abubuwa. Abin da zan iya fadi yanzu shine shugaban kasa ya kusa dawowa kuma mutane zasu fuskanci canji mai ban mamaki.”

KU KARANTA: An hana sayar da giya, karuwanci a Zamfara

" Kana kuma ina son in bayyana cewa matasan Arewa ba zasu taba yarda irin abinda ya faru lokacin marigayi Umaru Musa Yar'adua ya sake faruwa a 2019 na, wajibi ne arewa ta cikasa shekaru 8 din ta.”

Kana kuma ya caccaki gwamnonin Arewa wanda sukayi shiru Kaman mushrikai basu magana domin kare muradun Arewa.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel