Wani Basarake ya haɗa baki da wasu ɓarayi don suyi garkuwa da shi a Legas

Wani Basarake ya haɗa baki da wasu ɓarayi don suyi garkuwa da shi a Legas

- Wani basarake a jihar Legas yayi asarar rawaninsa

- Basaraken yayi asarar rawanin nasa ne bayan ya hada baki da wasu barayi don suyi garkuwa da shi

Gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya tsige wani basarake a jihar Legas wanda ya hada baki da wasu yan fashi da su kayi garkuwa da shi a ranar 5 ga watan Yuli a unguwar Ikosi-Isheri.

Gwamnan ya amince da sallamar Basaraken mai suna Cif Yusuf Ogundare a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli cikin wata takarda daya fitar mai lamba OLGAS.83/S./Vol.1, wanda ya aika ma shugaban karamar hukumar Ikosi-Isheri.

KU KARANTA: Dan ƙwallo ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa har lahira (HOTUNA)

Wasikar data samu sa hannun kwamishinan kananan hukumomi tace “An umarce ni in sanar da sallamar Sarkin Shangisha, Cif Yusuf Ogundare daga sarautansa.” kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Wani Basarake ya haɗa baki da wasu ɓarayi don suyi garkuwa da shi a Legas

Basarake Yusuf Ogundare da kaninsa Adams

Jami’an Yansandan jihar Legas ne suka kama Cif Yusuf tare da kaninsa Mohammed Adams wanda suka hada baki tare da shi domin ayi garkuwa dashi a ranar 11 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan kungiyar Asiri na kashe matasa a Legas, Kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel