Danjuma da wasu dattawan kirista sun yi Allah wadai da gwamnatin Buhari

Danjuma da wasu dattawan kirista sun yi Allah wadai da gwamnatin Buhari

- Kungiyar dattawan kirista na kasa ta kalubalanci gwamnatin shugaba Buhari

- Kungiyar ta zargi gwamnatin Buhari kan rikicin kabilanci da ta addabi kasar yanzu

- Dattawan sun bukaci gwamnati ta dawo da karatun addini a makarantu

Kungiyar dattawan kirista na kasa wato National Christian Elders Forum (NCEF), ta zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan rikicin kabilanci da ta addabi kasar yanzu da kuma yunkurin ballewa daga Najeriya da wasu yanki ke kokarin yi.

Dattawan wanda ya hada da tsohon babban jami'an sojojin kasar, ciki har da tsohon ministan tsaron kasar, Theophilus danjuma, sun yi Allah wadai ta yadda gwamnati ta kasa magance rikicin Fulani makiyaya da manoman, dattawan sun yi gargadin cewa tsattsauran ra'ayi wani ajanda na ‘yan jihadi.

Dattawan sun hadu ne a Abuja a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli. Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron sun hada da Mista Danjuma, Solomon Asemota, Joshuwa Dogonyaro da kuma Zamani Lekwot dukan su janar masu ritaya, Musa Ihonde, kuma Chukwuemeka Ezeife.

Danjuma da wasu dattawan kirista sun yi Allah wadai da gwamnatin Buhari

Tsohon ministan tsaron Najeriya, Theophilus danjuma

NCEF ta kuma nuna rashin gamsuwarta ga wasu gwamnatocin jihohi a kan kwace filayen ‘yan kasa domin kiwon dabbobin, inda suka zargi gwamnatocin da fifita wasu bangare.

KU KARANTA: Zargin rashin jituwa tsakanin Osinbajo da Buhari da Ministoci, Lai Muhammed yayi karin haske

Dattawan sun ci gaba da cewa: "Idan dole ne samar wa Fulani makiyaya wajen kiwon dabbobi, toh ya kamata a bada dajin Sambisa a matsayin filin kiwon dabbobin su”.

Kungiyar ta yi kira a kan dawowar da karatun addini a makarantu, ta kuma nuna goyon baya kan kira ga sake fasalin kudin mulkin kasar a halin yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel