Kotu ta yanke ma wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke ma wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Kotu ta zartarwa da matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Ya hada kai da wasu mutane biyu

- Sun yi sanadiyyar rasa ran wani mutum

Wata babban Kotu a Jahar Gombe ta yankewa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya kan tuhumar sa da laifin kisan kai.

An gurfanar da Umar Abdullahi, wanda aka fi sani da Gaso, mai shekara 25, mazaunin garin Gombe, a gaban kotu akan zargin hadin kai na aikata laifi da sandiyyar rasa ran wani mutum da suka yi.

Ana zargin sa da hadin kai da yayi da wasu samari biyu, Daddy da Bashir, da kashe wani mai suna Saidu Mukhtar.

Kotu ta yanke ma wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke ma wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta sami labarin cewa, a shekarar 2014, sun hada kai su ukun dauke da kayan makamai, suka kaiwa Mukhtar hari da sare-sare a unguwar shanu, kusa da tashar Dukku a Gombe. Wanda yayi sanadiyyar rasa ran sa. Samarin sun jiwa Mukhtar mummunan rauni wanda ya sa ya rasa ran sa a nan take.

Barista Maryam Ahmad ta shaida wannan laifi ya saba dokar shari’a. Gaso da aka fara gurfanar wa a gaban Kotu ya musa tuhumar da ake masa. Hakan ya sa Barista Maryam samar da shaidu da suka bada shaida akan laifin da ya aikata da makaman da suka yi anfani da su wajen kashe Mukhtar.

KU DUBA: Ministar kudi tayi amai ta lashe

Bayan bincike da Kotu tayi, an same samarin uku da aikata laifin kisan kai da ake tuhumar su da shi. Justice Beatrice ta shaida Barista Maryam ta bada kwararen hujjoji da suke a cikin kundin shari’a, hakan ya sa ta zartarwa da Gaso hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel