Masu yakar Buhari tamkar suna yaki da Najeriya ne – Shugaban jam’iyyar APGA

Masu yakar Buhari tamkar suna yaki da Najeriya ne – Shugaban jam’iyyar APGA

Dakta Ike Oye, shugaban jam'iyar APGA ya yi Allah wadai da masu yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari fatar mutuwa.

A cewar shugaban jam’iyyar ta APGA, shugaban kasar zai samu damar aiwatar da kyakkyawan nufi ne idan har ya samu yarda da goyon bayan al’umman kasar.

Ya kara da cewa dukkan masu yakar shugaba Buhari tamkar suna yakar kasar Najeriya ne. sannan kuma yace idan shugaban kasar yam utu gobe toh lokacin sa ne yayi kuma babu wanda zai guje wa mutuwa, kowa ma zai mutu idan lokacin sa ya yi, don haka a daina gaggawa domin Allah kadai ne ya san gawar fari.

KU KARANTA KUMA: Ibo ne zai zama shugaban kasa a zaben 2019Ibo ne zai zama shugaban kasa a zaben 2019

Ya ce: “Shugaba Buhari zai yi abun kirki ne idan har ya samu amincewar yan kasa. Dukkan maƙiya masu yakar Buhari daga ko wanne ɓangare, walau hagu, dama ko tsakiya, ba shugaba Buhari suke yaƙa ba. Suna yaƙi da Nijeriya ne.

"Idan Buhari ya mutu gobe, ba makawa lokacin shi ne ya yi, dukkan mu zamu mutu. To menene na gaggawa?

"Inada yaƙinin cewar idan Buhari ya mutu yau, to ya mutu ne akan tafarkin nemarwa talakawan ƙasarsa mafita, kuma idan ya mutu ya mutu domin mu ne saboda mu muka ba shi matsalar da ta yi sanadiyarsa.”

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel