An kama wanda ya yiwa Namadi Sambo cinne

An kama wanda ya yiwa Namadi Sambo cinne

- Hukumar ICPC ta kama wani mutumi mai suna Abubakar Sani Chindo

- Ta kama shi ne bisa laifin kai rahoton karya a kan tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo

- A baya jami’an tsaro sun kai farmaki gidan tsohon mataimakin shugaban kasar bayan sun samu rahoton cewa ya boye wasu makudan kudade

Hukumar dake yake da cin hanci da rashawa mai zaman kanta wato ICPC ta yi ram da wani mutumi mai suna Abubakar Sani Chindo sannan ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa laifin bayar da rahoton karya a kan tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo.

A cewar rahoton, Chindo ya yi ma tsohon mataimakin shugaban kasar cinne bayan ya sanar da cewa Sambo ya boye makudan kudade a gidansa dake Kaduna garin gwamna.

Amma dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumar sa a kai, sai dai alkalin kotun da aka gurfanar da shi, mai shari’a MT Aliyu ba ki yarda ya bayar da belin sa.

An kama wanda ya yiwa Namadi Sambo cinne

An kama wanda ya yiwa Namadi Sambo cinne

Sannan kuma zai fuskanci hukuncin zama a gidan yari har na tsawon shekara goma idan har aka same shi da laifi bayan bincike.

KU KARANTA KUMA: Ministar kudi ta yi amai ta lashe

Idan dai zaku tuna a ranar 28 ga watan Yuli NAIJ.com ta rahoto cewa jami’an tsaro sun kai farmaki gidan tsohon mataimakin shugaban kasar bayan sun samu rahoton cewa ya boye wasu makudan kudade.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel