Hukumar yansanda zata aika yansanda 5,000 don bada tsaro a zaben kananan hukumomi a jihar Kebbi

Hukumar yansanda zata aika yansanda 5,000 don bada tsaro a zaben kananan hukumomi a jihar Kebbi

- Yansanda 5,000 za'a aika don tsaro a gudanarda zaben kananan hukumomin jihar

- Za'a hana zirga-zirga daga karfe shida na safe zuwa shida na yamma a ranar zaben

Hukumar yan sanda na yankin Jihar kebbi, sun bada bayanin zasu aika yansanda 5,000 domin bada tsaro a gudanarda zaben kananan hukumomin jihar a sha bakwai ga watan yuli.

Mai magana da yawun hukumar, DSP Mustapha Suleiman, ya sanarwa da manema labarai a yau Juma'a a birnin kebbi cewa yansanda shirye suke don hada kai da dukkan jami'an tsaro na jihar baki daya don ganin kyautatuwar zaben.

Hukumar yansanda zata aika yansanda 5,000 don bada tsaro a zaben kananan hukumomi a jihar Kebbi

Hotunan yansandan dake shirin bada tsaro

A karin bayaninsa, ya nuna za'a hana zirga-zirga daga karfe shida na safe zuwa shida na yamma a ranar zaben, kuma ya shawarci jama'a dasu kasance masu bin wannan dokar.

Ya bada tabbacin cewar yansanda da sauran jami'an tsaro zasu tabbatar da cikarken tsaro don bawa jama'a masu yanci yin zabe a cikin aminci tareda maganje kowacca irin barazanar da ka iya tasowa.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na kirkiro jihohi a Najeriya – Gowon

Suleiman ya nema daga mazauna jihar a nakaltowar NAIJ.com dasu bada cikakken hadin kai daga bangarensu.

Zaben dai zai kasance ne a tsakanin kananan hukumomi 21 na jihar a Ranar Lahadi mai zuwa.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon Ambaliyan Ruwa a Legas da ra'ayoyin mazaunan Legas akan ambaliyan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel