Ambaliyar ruwa ya ci gidaje a Birnin Kebbi

Ambaliyar ruwa ya ci gidaje a Birnin Kebbi

Rahotanni sun kawo cewa ambaliyar ruwa ya yi mummunan barna a yankin Rafin Atiku dake birnin Kebbi, wanda yay i sanadiyar hallaka gidaje da dama a yankin.

A cewar rahoton wannan ba shine karo na farko da ake samun wannan annoba ta ambaliyar ruwa a yankin ba saboda rashin magudanar da ruwa zai bi a yankin, don ko a bara sai da aka fuskanci wannan matsala ta ambaliyar ruwa.

A wannan karo an samu ambaliyar ne bayan an dauki tsawon sa’o’I uku ana zuba ruwan sama kamar da bakin kwarya, sannan kuma wadanda abun ya shafa sunyi kira ga gwamnati da ta kawo masu agajin gaggawa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnati za ta share wa jihohi 15 da ambaliyar ruwa ta shafa hawaye da biliyan 1.6

A baya dai NAIJ.com ta rahoto cewa mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya umurni ministar kudi, Kemi Adeosun da ta gaggauta fitar da naira biliyan 1.6 daga babban bankin kasar, CBN ta rabawa jihohi 15 da ambaliyar ruwa na kwanan na ta shafa.

Jihohin da suke fama da ambaliyar ruwan sun hada da; Ekiti, Osun, Akwa Ibom, Kebbi, Neja, Kwara, Ebonyi, Enugu, Abiya, Oyo, Legas, Filato, Sakkwato, Edo da Bayelsa.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan da kammala taron majalisar zartarwa.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel