Kano za ta rasa matsayinta idan Kabilar Ibo suka bar jihar-Ganduje

Kano za ta rasa matsayinta idan Kabilar Ibo suka bar jihar-Ganduje

- Ikpeazu ya ziyarci jihar Kano dan mika taza’aziyan sa na rasuwan Danmasanin Kano Alhaji Maitama Sule.

-Hadin kan Najeriya dole ne-gwamna Ikpeazu

- Kano jiha ce mai dimbin tarihi wajen karban baki

Gwamanan jihar Kano Abullahi Ganduje , a ranar laraba yace jihar Kano ta kai masayin ta na babbar Jigo a kasuwanci, saboda gudumawan da Iyamurai da wasu kabilun sassan kasan suka bada.

Ya kuma baiwa manyan kasan laifi akan kiran da wasu sashen yan kasa kai yi na rabuwa.

Ganduje yayi wa’anan kalaman ne lokacin da Gwamnan Jihar Abia Dr Okezie Ikpeazu ya ziyarci jihar dan mika ta’aziyan sa na rasuwan Danmasanin Kano Alhaji Maitama Sule.

Kano za ta rasa matsayinta idan Kabilar Ibo ta bar garin-Ganduje

Kano za ta rasa matsayinta idan Kabilar Ibo ta bar garin-Ganduje

Akan manyan kasan nan, ya kalubalance su da cewa “za a samu mutun mai ilimi amma bai da hikima ; wannan shine abun da ke faruwa da manyan kasannan na yanzu. kuma Shi yasa muke da yan fafutukar neman yanci a wani bangaren kasan. Babu hikima a wannan alamarin gaba daya."

Ku Karanata:https://hausa.naija.ng/1114744-makarfi-ya-koma-aiki-a-sakateriyar-pdp.html

“ Zuwan ka jihar mu dan mika ta’aziya, ya nuna soyayyar da ke tsakanin jama'a a fadin kasan nan. Kuma alama ce na tabbatuwar hadin kan kasa."

Ganduje ya kara da cewa : “Abun ya mana zafi sosai lokacin da wasu ke kira da araba kasan. Lokacin da akaba iyamurai wa’adin barin Arewa. Mu a Kano mun barranta da wannan mummunan kira. Kuma mun zauna mun tattauna da matasan mu da kuma wa’anda ba yan jihar ba, kan babu wanda zai bar jihar Kano da arewa baki daya."

“ Mun cire iyakan ‘dan asalin jiha’ saboda duk wan da yake zama a Kano ya zama dan gari mai yanci Kaman haifaffen jihar. Kano jiha ce mai dimbin tarihi wajen karban baki.

Kano wadda take jijiyan kasuwanci ce a Arewa da nahiyan Africa na yamma ta samu wannan matsayin ne tare da taimakawan wasu kabilu musamman Iyamurai. Idan wannan shine mutuncin mu mai yasa muke son karya ginshikin kasuwancin kasan.

“Muna bukutan hadin kan juna dan samun cigaba. Al’umman kasar nan na bukatan kowa da kowa. Kasar Amurka ta zama babbar al'umma ce saboda karban mutane da tayi daga sassan duniya daba-daban, kuma ko wanne yazo da irin nashi ilimin shiyasa tafi kowani al’umma ci gaba wajen kimiya da fasaha."

A jawabin, Ikpeazu yace hadin kan Najeriya dole ne.

Yace :“Matsayin sa akan wannan al’amarin shine hadin kan Najeriya yazama dole. Nayi shekara bakwai ina karatu a Jami’an Maiduguri tun ina dan shekara 16 har nayi digiri na biyu acan. Bayan haka nayi aiki a jihar Legas. Na ga kowani sashen kasan, wannan dalilin yasa naga mahimmancin zaman tare.

Naga fa’idan hadin kan al’umma daban-daban , abin da zan iya fadi game da haka shine wani Karin Magana da ake cewa “hanun ka baya rubewa ka yar. Idan akwai wani matsala, kamata yayi a zauna a tattauna dan dinke barakan. Bana tsammanin fasa kwan zai sa mu, cin ma burin mu."

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel