Ambaliyar ruwa a Indiya ya halaka Mutane 83

Ambaliyar ruwa a Indiya ya halaka Mutane 83

- Ambaliyar ruwa a indiya ya halaka mutane kimanin 83 da dabbobi uku da ake kewar batansu a matattarar dabbobi mafi girma a duniya

- Kungiyar kai doki da agaji da ke kutsawa don zuwa ceto mutane a yankunan sun bada bayanin cewa mutane miliyan biyu ne suka rasa muhalli

Ruwan da ya auku sakamakon ruwan sama mai karfi da akayi a hayiryikan Assam, Arunachal Pradesh, Nagaland da Manipur a sati biyu da suka wuce. Ruwan kuma yayi sanadin sabular yankoki na kasa mai kama da girgiza.

Masu bada bayani sun nuna cewa a takaice, kuma a gaba daya, kimanin mutane miliyan biyu ne suka rasa muhalli a guraren.

Ambaliyar ruwa a Indiya ya halaka Mutane 83

hoton wani yanki guraren da ambaliyar ya shafa

A bayanin Sarbananda Sonowal, Ministan Yankin Assam kamar yarda NAIJ.com ta nakalto, yace; “Yankin Assam shine wanda bala'in yafi shafa a yayinda aka samu lissafin rasa rayuka 53, tareda rasa muhallin mutane miliyan biyu".

Ta kara da cewa Kungiyar kai doki da agaji akafa suke kutsawa don zuwa ceto mutane a yankunan.

KU KARANTA: Makarfi Ya koma aiki a Sakateriyar PDP

Firiministan Narendra Modi ya aika tawagar gwamnatinsa a karkashin jagorancin Kiren Rijiju, don bibitar lamarin da ganin abubuwan da ya dace gwamnatinsa tayi.

Borin ruwan rafin Brahmaputra ya kai farmaki matattarar zoo na dabbobin Kaziranga a Assam, kuma ya tursasa dabbobi neman mafaka wa rayuwarsu a gurare mabanbanta.

Matattarar dabbobin Kaziranga National Park, wanda ke karkashin kungiyar duniyan UNESCO world heritage, ya kasance dauke da dabbobi kimanin 2,500 narhinos daga cikin 3,000 dake duniya baki daya. Ta kara da cewa kusan dabbobi 60 ne suka rasa rayukansu a sakamakon ambaliyar ruwan saman.

Ku biyomu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon Ambaliyar Ruwan Legas da tsokacin mutane akai

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel