Ministar kudi ta yi amai ta lashe

Ministar kudi ta yi amai ta lashe

Rahotanni sun kawo cewa ministar kudi na tarayyar Najeriya, Misis Kemi Adeosun ta yi amai ta lashe, bayan ta sanar da cewa ya zama lallai gwamnatin tarayya ta nesanta kanta daga zancen ciyo bashi don neman bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ta ce abun daya kamata shine gwamnati ta wadata hanyoyin tara kudaden shiga a maimakon ciwo bashin.

Sai ga shi a yanzu kuma ta sauya akalar zancen ta, a wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan ma’aikatar kudin tarayya, Salisu Dambatta, ta bayyana cewa kasar Najeriya bata da wata mafita da ya wuce ciwo bashi don ta samu zarafin inganta fannin tattalin arziki.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa ministar Kudi, kemi Adeosun, tayi gargadin cewa Najeriya baza ta iya kara ciwo bashi ta zuba a kasafin kudi ba.

Ministar kudi ta yi amai ta lashe

Ministar kudi ta yi amai ta lashe

KU KARANTA KUMA: Najeriya baza ta iya kara ciwo bashi a waje ba, inji Kemi Adeosun, ministar kudi

Ta koka kan karancin kasafin kudi bazai wadatar da aikata muhimman ayyuka ba a Kasar, sai dai a nemi hanyar samun kudi a cikin gida da za a zuba a kasafin kudi. Najeriya ta tsaida bashin da ta shirya ciyowa daga Bankin Duniya na $2 biliyan.

Adeosun ta bayar da shawarar Najeriya bazata sake ciyo bashi ba. Mai da hankali akan haraji shi ne dai-dai, duk da shi baikai karbar bashi saurin tafi da Kasa ba. Amma hakan zai hana Kasar fadawa tarkon bashi.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel