Dogara: An bukaci canja kundin tsarin mulki na 1999

Dogara: An bukaci canja kundin tsarin mulki na 1999

- An bukaci canja kundin tsarin kasa

- Babban jojin Najeria ya gabatar da sabon tsarin

- Dogara yayi fari ciki da wannan tsari

A ranar larabar da ta gabata ne shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya bayyanawa manema labarai cewa matukar ana son sauya Najeriya sai an canja kundin tsarin dokar kasa na 1999 domin kawo cigaba a kasar nan.

Dogara: An bukaci canja kundin tsari na 1999

Dogara: An bukaci canja kundin tsari na 1999

Dogara ya shaida cewa majalisar dattawa ba za su kawo wata tangarda ba wajen canja kundin tsarin na kasa, sai dai yace canja kundin tsari ba abu ne karami ba, dole sai an bi abin daki-daki.

Yace majalisar wakilai da dattawa a shirye suke don ganin an canja kundin tsarin matukar an samu yarjejeniyar al’ummar kasar nan.

An fara tattaunawa a kan canja kundin tsarin na kasa a lokacin da babban jojin Najeriya Walter Onnoghen ya gabatar da tsare-tsraen a gaban majalisar dattawa.

KU KARANTA: An fille kan wasu 'yan'uwa 2 a Fatakwal (Hotuna)

Tsare-tsaren da ya gabatar sun hadarda: canjin shekarun ajiye aiki da shiga, rage lokacin da ake dauka ana shari’a a kotu da kuma sauran tsare-tsare wanda suka danganci gudanarwar shari’ar kasar nan.

Shugaban majalisar wakilai yayi murna da wannan tsari kuma yace a shirye suke ta bangaren su don ganin tabbatuwar wannan abu, domin zai kawo cigaba a kasar nan baki daya.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel