Wani fasinjan Jirgin saman Emirates ya mutu daga isarsu Legas

Wani fasinjan Jirgin saman Emirates ya mutu daga isarsu Legas

- Fasinjan dan Najeriya ya mutu ne bayan doguwar jingina da yayi a kan kujerarsa a cikin jirgin

- Mamacin, Gwamnan Lion's Club ya taso ne tun daga kasar Amurka tareda Matarsa

Mutumin dan Najeriyan ya mutu ne a jirgin a ranar Laraba da ta wucea isarsu filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Jihar Legas.

Jirgin saman Emirates din da fasinjan ya mutu a cikinsa

Wani fasinjan Jirgin saman Emirates ya mutu daga isarsu Legas

Bincike da bibitar bayanai sun nuna cewa sunan wanda ya mutun a jirgin saman mai Lamba EK783 (DX) Olusola Dada wanda keda lambar fasfot A04501199

Mai magana da yawun filin jirgin saman na Yansanda,Joseph Alabi ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Dangote zai zuba kudi kimanin biliyan $4.6 a harkar noma

Mr. Alabi, Mataimakis sufurtanda na yansanda yace sanarwar ta iso garesu ne bayan likitoci sun tabbatar da mutuwar fasinjan

Mamacin da ya taso tun daga kasar Amurka tareda Matarsa ya mutu ne tun kimanin karfe 3.55p.m. a yayin isarsu.

NAIJ.com ta nakalto cewa likitoci sunyi iya bakin kokarinsu gun ganin sun ceto ransa, amma basu samu yin hakanba, sun sanar da mutuwar tasa ne a dai dai karfe 5.34 p.m.

wasu karin bayanai sun nuna cewa mamacin ya kasance Zababben gwamna ne na yankin na Babbar Kungiyar Lions Club International, District 404 A1.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Shawarar sulhu tsakanin IPOB da Gwamnati da wani soja ya bayar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel