Atiku Bagudu ya yabawa sarakunan gargajiya kan samar da zaman lafiya

Atiku Bagudu ya yabawa sarakunan gargajiya kan samar da zaman lafiya

- Gwamnan jihar Kebbi ya yabawa sarakunan gargajiya kan gudumawar su wajen samar da zaman lafiya a Jihar

- Gwamnan ya ce sarakunan gargajiya sun taka rawar gani wajen kawo karshe rikici tsakanin Fulani makiyaya manoma

- Bagudu ya umurni dukan kananan hukumomi da su aika sakamakon ganawarta na wata-wata ga ofishinsa

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya yabawa sarakunan gargajiya a lokacin da ya ziyarci fadar sarakunan Gwandu, Argungu, da kuma Hakimin Aliero da Gwandu da Jega da Maiyama a matsayin wani ɓangare na yakin neman zabe a zaben kananan hukumomi wanda za a yi a wannan Asabar, 15 ga watan Yuli.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, gwamnan ya yabawa sarakunan kan rawar da suka taka wajen kawo karshe rikici tsakanin Fulani makiyaya manoma ta hanyar tattaunawa, gwamnan yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da girmamawa sarakunan gargajiya.

Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce dole ne yanzu kowane karamar hukuma a jihar Kebbi ta mika sakamakon ganawarta na wata-wata ga ofishinsa, kuma ya ce kasawa da hakan zai sanadiyar dakatar da biya albashin majalisar kananan hukumomin da abin ya shafa.

Atiku Bagudu ya yabawa sarakunan gargajiya a Jihar

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu

Da yake jawabi, sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Ilyasu Bashar, kuma mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama'ila Muhammadu Mera sun nuna goyon baya da kuma biyayya ga gwamnati.

KU KARANTA: Ibo ne zai zama shugaban kasa a zaben 2019

A fadar Lammen Augie, Alhaji Adamu Augie, Hakimin Gwandu, Alhaji Bello Mai-Wurno, Aliero Alhaji Salisu Mohammed, Jega, Alhaji Arzika Bawa Sarkin Kabi Jega, Maiyama, Alhaji Adamu Aliyu Maiyama da sarakunan gargajiya duk sun gode wa gwamnatin jihar domin aiwatar da ayyukan ci gaba daban-daban a mazarautar su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel