Shugabancin PDP: Har yanzu ina cikin kaduwa, inji Ali Modu Sheriff

Shugabancin PDP: Har yanzu ina cikin kaduwa, inji Ali Modu Sheriff

- Kotun daga ke sai Alllah-ya-isa dai ta yi atali da shugabancin Ali Modu

- Yace lauyoyinsa har yanzu basu yi masa bayani ba

- Yayi kira ga magoya baya su kara hakuri

A jiya ne dai wata gingimari shudiya ta zo ta tattara komatsan saukakken shugaban jam'iyyar PDP daga shalkwatar su ta Wadata Plaza dake babban birnin tarayya a Abuja, wanda hakan ya share fagen shigar sabon shugaba Ahmed Makarfi, Sanata na Kaduna, kuma tsohon gwamna.

Shi dai Ali Modu Sheriff na Borno, bai sami halartar zaman kotun ba, kuma yace har yanzu bai sami cikakken rahoto daga lauyoyinsa ba, amma yace wannan hukunci ya zo masa bagatatan, inda har yanzu yana cikin kaduwa da wannan sauyi.

Shugabancin PDP: Har yanzu ina cikin kaduwa, inji Ali Modu Sheriff

Shugabancin PDP: Har yanzu ina cikin kaduwa, inji Ali Modu Sheriff

A ta bakin hadiminsa mai yada labaransa dai, Bernard Mikko, suna kan baiwa magoya bayansu hakuri sannan suna jiran lauyoyinsu su basu cikakken bayani.

Ana saka ran da yawa daga cikin magoya bayansa dai zasu iya komawa jam'iyya mai mulki ta APC, duk da yafiya da sabon shugaba MAkarfi yayi alkawarin yiwa Modu Sheriff wanda a cewarsu ya bata wa jam'iyyar loaci har shekaru biyu.

DUBA WANNAN: Zazzafan martani ga Nnamdi Kanu daga Orji Uzor Kalu

Sanarwar da ta fito daga bangaren shugaban mai murabus dai, tayi kira ga magoya baya da su yi hakuri, su kuma yi ta yi wa Najeriya addu'a, su kuma saurari mataki da zasu dauka na gaba.

'Har a yanzu dai muna kira ga jam'iyya da ta yi adalci ta bari talakawa su tafiyar da jam'iyya, su kuma zama su suke iya zabo shuwagabanninsu' sanarwar ta sake cewa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel