Ta'addancin wasu fulani makiyaya a jihar Edo ya jawo wa sauran Hausa/Fulani sa-idon gwamnati

Ta'addancin wasu fulani makiyaya a jihar Edo ya jawo wa sauran Hausa/Fulani sa-idon gwamnati

- Ana samun hare-haren makiyaya a wasu jihohin kudancin kasar nan

- Gwamnatin jihar Edo zata dauki babban mataki

- Duk wani wanda ke zaman jihar daga arewa za'a yi masa katin shaida

Ana zaman dar-dar a da yawa daga kauyukan jihar Edo, inda wasu ma tuni sun daina zuwa gonakinsu saboda matsalar makiyaya da ake zargi da fashi da fyade ga mata da manoma a wasu yankuna na jihar.

Ta'addancin fulani makiyaya a jihar Edo ya jawo wa sauran Hausa/Fulani sa-idon gwamnati

Ta'addancin fulani makiyaya a jihar Edo ya jawo wa sauran Hausa/Fulani sa-idon gwamnati

A yanzu dai gwamnan jihar Obaseki yace jihar ta gaji da jiran gwamnati tarayya, don haka zata dauki babban mataki domin magance matsalar.

A sabon shirin, za'a yi wa duk wani mazaunin yankin wanda ba dan asalin jihar ba, katin shaidar zama, inda ya ce hakan zai yi saurin fitar da bako mai mugun nufi kan jama'a.

DUBA WANNAN: Orji Kalu ya mayar wa da Kanu na IPOB martani mai zafi

A da yawa daga kasashen duniya dai, yin hakan wani babban abin tsoro ne, wanda zai iya jawo wa baki tsangwama da harara, da kuma dora wa wata kabila laifin wasu masu laifi walau daga kabilar tasu ko a'a.

Ita dai gwamnatin tace Hausawa da Fulani zata yi wa wannan rajistar, amma kawai domin zabe baki masu isowa a kwanakin nan ne, wadanda yawanci fashi da makami ke kawo su jihar.

A cewar gwamnan, irin haka anyi a Kaduna da jihar Legas, kuma shirin ya sami nasara wajen dakile munanan hare-hare na bakin haure daga wasu kasashen makota.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel