Zargin rashin jituwa tsakanin Osinbajo da Buhari da Ministoci, Lai Muhammed yayi karin haske

Zargin rashin jituwa tsakanin Osinbajo da Buhari da Ministoci, Lai Muhammed yayi karin haske

- Ana zargin wasu ministoci da kin biyayya ga shugaba Osinbajo

- Lai Muhammed yayi karin haske

- Wasu ministoci dai suna tsallake Osinbajo zuwa Ingila domin wasu batutuwa na gwamnati

A taro na tattaunawa kan harkokin inganta sufurin jiragen sama a jihar Legas da aka yi jiya, Ministan yada labarai yayi karin haske kan batun wai ko akwai rashin jituwa tsakanin Osinbajo Mukaddashin shugaba Buhari da Buharin, dama zargin kin yi wa Farfesan biyayya a gwamnati tsakanin ministoci.

Zargin rashin jituwa tsakanin Osinbajo da Buhari, da Ministoci, Lai Muhammed yayi bayani dalla-dalla

Zargin rashin jituwa tsakanin Osinbajo da Buhari, da Ministoci, Lai Muhammed yayi bayani dalla-dalla

A baya dai an sami rahotanni da suka nuna wasu ministoci sun gwammace su hau jirgi suyi tattaki har Ingila saboda su zagaye Yemi Osinbajo din su samo sahalewar shugaba Buhari kan wasu ayyuka nasu, amma wai shugaba Buharin ya gwale su ya koro su gida.

A cewar tahoton dai, shugaban yayi fushi inda har yace ba'a shugaba biyu a gwamnatinsa. Ko dai su kyale shi ya yi jinya, wadda ita ta kai shi kasar waje, ko kuwa su je wurin mukaddashinsa su taya shi aiki.

A irin wadannan zantuka ne aka yi wa Ministan yada labarai tambaya shin ko akwai tasgaro kan yadda tsarin gwamnatinsu ke tafiya, inda yace 'gutsuri-tsoman 'yan siyasa ne da baka raba dimokuradiyya da shi'

DUBA WANNAN: Zumudi kan Biafra, Orji Kalu ya maida martani ga Kanu

A cewar Minista, su gwamnatinsu a hade take wuri guda, babu wani tangal-tangal da suke ji, kawai dai masu son sai sun kirkiri abin fada ne ana zaune kalau.

'Mu aiki muka saka a gaba, ina farin ciki da wannan gwamnati tamu a Najeriya, domin ayyukan alheri muka sa a gaba, na yada zuki-ta-malle da zaidauke mana hankali' Ya sake fadi.

Ana ganin dai sanin wasu manyan 'yan siyasa cewa a shekarar 2014, Yemi Osinbajo kwamishina ne a jihar Legas, don haka bai kai wani matsayi da zai zama babban gwaska mai iya tafiyar da kasa kamar Najeriya ba, duk da namijin kokari da shugaban yake yi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel