Osinbajo ya yi ganawar sirri tare da manyan ýan majalisa

Osinbajo ya yi ganawar sirri tare da manyan ýan majalisa

- Kakakin majalisa, Yakubu Dogara, da wasu manyan jamiái na majalisa sun gana da Osinbajo don tattaunawa a cikin fadar shugaban kasa

- Wasu daga cikin hadiman shugaban kasa ma sun halarci taron wanda ake ganin yana daga cikin kokari da akeyi na sasanta barakar dake tsakanin bangaren dokoki da bangaren zartarwa

Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya gudanar da wata ganawa ta sirri tare da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da sauran manyan ýan majalisa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an gudanar da ganawar ne a daren ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, a gidan Osinbajo. Aguda House, a cikin fadar shugaban kasa Abuja da misalign karfe 10 na dare.

Ganawar wanda ake ganin yana daga cikin kokari da ake yi na dinke barakar dake tsakanin bangaren dokoki da bangaren zartarwa ya samu halartan wasu hadiman shugaban kasa gurin raka mukaddashin shugaban kasar.

Osinbajo ya yi ganawar sirri tare da manyan ýan majalisa

Osinbajo ya yi ganawar sirri tare da manyan ýan majalisa

NAIJ.com ta tuna cewa ýan majalisar wakilai a ranar Talata, 11 ga watan Yuli, sun ba Osinbajo waádin kwanaki bakwai kan ya rantsar da ministoci biyu daga jihohin Gombe da Kogi.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun kuma kai hari a iyakar Kamaru da Najeriya, mutane 16 sun mutu

Osinbajo na da Baraka da majalisar dattawa wanda a kwanan nan suka yi kira ga dakatar da suk wani nade-naden mukamai na shugaba Muhammadu Buhari kan wani furuci da mukaddashin shugaban kasar ya yin a cewa nade-naden bangaren zartarwa baya bukatar amincewar ýan majalisa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel