‘Yan jam’iyyar PDP masu biyayya ga Sheriff na shirin barin jam’iyyar

‘Yan jam’iyyar PDP masu biyayya ga Sheriff na shirin barin jam’iyyar

- Kotun koli ta tabbatar da bangaren Ahmed Makarfi a matsayin ainahin shugaban jam’iyyar PDP a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli

- Hukuncin kotun na iya janyo mutane da dama su sauya sheka daga PDP

- An rahoto cewa masu biyayya ga Sheriff sun fara shirin barin jam’iyyar

Wani dan jam’iyyar APC a jihar Imo, Jones Onwuasoanya, ya ba da tsokaci kan cewa wasu ‘yan PDP a jihar na shirin komawa APC saboda hukuncin kotun koli na tabbatar da Makarfi a matsayin shugaban jam’iyyar ta kasa.

NAIJ.com ta rahoto a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli cewa kotun koli ta tabbatar da bangaren Makarfi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na gaskiya.

Yayinda jiga-jigan jam’iyyar da dama ke ta kira ga sasanci bayan hukuncin kotu, wasu daga cikin masu biyayya ga Sheriff na iya barin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Ibo ne zai zama shugaban kasa a zaben 2019

Onwuasoanya ya lissafa ‘yan siyasan kasa a matsayin wadanda ka iya komawa APC.

1. Sanata Hope Uzodinma

2. Honourable Goodluck Opiah

3. Nnamdi Anyyaehie

4. George Eguh

5. Enyinnaya Onuegbu

6. Emmanuel Orie

7. Nnanna Igbokwe

8. Bright Nwelue

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel