An fille kan wasu 'yan'uwa 2 a Fatakwal (Hotuna)

An fille kan wasu 'yan'uwa 2 a Fatakwal (Hotuna)

- An fille kai wasu ‘yan’uwa biyu, Ifeanyi da kuma Emeka Wobo a Fatakwal

- Har yanzu ba gane wadanda suka aikata danye aikin ba

- Wadannan 'ya'ya biyu ne kawai yara mazan da marigayi Cif Oliver Wobo ya haifa

Wasu da ba san ko su wanene sun halaka da kuma fille kai wasu 'yan'uwa biyu, Ifeanyi da kuma Emeka Wobo, mazaunar al’umman Rumuokparali a karamar hukumar Obio Akpor da ke Jihar Ribas.

Jami’an ‘yan sandan jihar ne suka gano ragowar jikin 'yan'uwan a kusa da Elekahia Housing Estate a Fatakwal babban birnin jihar a ranar Talata, 11 ga watan Yuli.

NAIJ.com ta ruwaito cewa 'yan'uwan sun shiga wani motar kasuwa daga Rumuokparali a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli da yamma, kafin jami’an tsaro ta gano gawawwakin su a washe gari.

An fille kan wasu 'yan'uwa 2 a Fatakwal (Hotuna)

'Yan'uwa biyu, Ifeanyi da kuma Emeka Wobo wadanda aka fille musu kai

Shugaban matasan yankin, Mista Pamoses Omah ya shaida wa majiyar NAIJ.com cewa labarin mutuwar ‘yan’uwan ya jawo hayaniya da kuma bacin rai a tsakanin al'ummar yanki.

KU KARANTA: Hausawa da Fulani sun kai karar Gwamnatin tarayya da jihar Taraba kara kotun kasa-da-kasa

Omah ya ce: " Wadannan 'ya'ya biyu ne kawai yara mazan da marigayi Cif Oliver Wobo ya haifa".

"Babu wanda ya san abin da ya faru da su, kawai a cinci gawawwakin ne a kusa da Elekahia Housing Estate".

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, DSP Nnamdi Omoni, ya tabbatar da al’amarin kuma ya ce tuni ‘yan sanda sun fara bincike a kan kisan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel