Kungiyar matasan jihar kogi ta kalubalanci gwamna Bello, ku karanta

Kungiyar matasan jihar kogi ta kalubalanci gwamna Bello, ku karanta

- Kungiyar matasan jihar Kogi ta kalubalanci gwamna Bello cewa ya gudanar da zaben kananan hukumomi idan ya san yana da jama’a

- Shugaban kungiyar ya ce ziyarar gwamnan zuwa wasu makarantu ba zai cece shi a zaben shekarar 2019 ba

- Austin, akwai isasshen lokaci na yin kamfen neman zabe

Shugaban wani kungiyar matasa na kasa wato Peoples Democratic Youth Frontiers, Usman Okai Austin ya kalubalanci gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello da ya gudanar da zaben kananan hukumomi idan ya san da cewa jama’a na son sa.

Austin, wanda ya bayyana haka a cikin sanarwar da aka bayar ga 'yan jarida a Lokoja, ya bayyana ziyarar gwamnan zuwa wasu makarantu a matsayin wasan yara, inda ya lura cewa wannan ba zai cece shi a zaben shekarar 2019 ba.

Shugaban kungiyar ya ce: “Akwai isasshen lokaci na yin kamfen neman zabe, ko mutanen jihar za su amince a sake zaben shi ko kuma za su ƙi, zamu gani a zaben shekara 2019, amma muna bukatar ya fito ya nuna farin jininsa”.

Kungiyar matasan jihar kogi ta kalubalanci gwamna Bello, ku karanta

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello

KU KARANTA: Dalilin da yasa na kirkiro jihohi a Najeriya – Gowon

A ziyarar gwamnan zuwa wasu makarantu, Austin ya bayyana shi a matsayin yaudara da kuma rashin adalci ga malamai makarantun da aka yi wa korar walakanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel