Hukumar EFCC tayi ram da wani Bawan Allah a Kaduna

Hukumar EFCC tayi ram da wani Bawan Allah a Kaduna

- Hukumar EFCC tayi ram da wani ‘Dan kasuwa a Garin Kaduna

- Ana zargin Umar Faruk da laifin karkatar da kudin wasu kwangila

- Wannan mutumi ya sha kwana da wasu kudi sama da Miliyan 100

Hukumar EFCC ta maka wani Umar Faruk da kamfanun sa a Kotu inda ake zarin sa da laifi har biyu. Daga ciki dai akwai zargin karkatar da wasu kudin kwangila da aka ba shi amma yayi mursisi.

Hukumar EFCC tayi ram da wani Bawan Allah a Kaduna

Hoton wanda ake zargi daga Hukumar EFCC

A yau dinnan ne dai babban Ofishin Hukumar na Yankin da ke Kaduna ya shigar da kara gaban Alkali M.T Aliyu bisa zargin karkatar da wasu makudan kudi ha N120,700,000 na kwangila da aka bada a kaf Kananan Hukumomin Jihar Kaduna.

KU KARANTA : Gwamnan Kaduna yayi babban bako yau

Hukumar EFCC tayi ram da wani Bawan Allah a Kaduna

Hukumar EFCC tayi ram wannan mutumi

Wannan mutumi Umar Faruk Salisu ya sha kwana da kudin aikin bayan an mika masa a hannu, ta kare ba kaya ba kudi. Alhaji Umar Darekta ne a wa Kamfani kuma ya karbi wannan Kwangila daga Gwamnatin Jihar a 2014 amma bai yi aikin ba. Yanzu dai an bada belin sa da sharuda.

Ku na ina wani Tsohon Shugaban Jami'ar Obafemi Awolowo OAU, Farfesa Anthony Elujoba ya wuce gidan kurkuku inda ake zargin sa da shan kwana da wasu sama da Naira Biliyan 1.4 lokacin yana rike da Makarantar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Evans ya tsrere daga hannun 'Yan Sanda ?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel