Kotun tarayya ta ci tarar lauyan Evans naira dubu ashirin (N20,000)

Kotun tarayya ta ci tarar lauyan Evans naira dubu ashirin (N20,000)

-Kotu ta gargadi lauyan Evans daya daina aikata laifin da ya saba wa dokan aikinsu

-Evans yayi kira da asake shi idan babu wani laifi akansa

-Baban Evans ya nemi hukuma da ta biyasu diyyar naira N300m saboda batancin da aka ma dan sa

Justice Abdulazeez Anka na Babbar Kotun Tarayya Legas ya maka wa mista Olukoya Ogugbeje lauyan shahararen mai garkuwa da mutane Chukwudumeme Unwuamidike wanda aka fi sani da evans tarar N20,000.

Jusice AbdulAzeez Anka, ya gargadi lauyan da ya daina aikata abun da ya saba wa dokan aikinsu.

Alkalin ya zartar da hukuncin ne bayan kai karar da lauyan Evans yayi zuwa ga hukumar kare yancin dan Adam, na cewa ana rike dashi ne ba'a bisa kai'da ba.

Kotun tarayya ta ci tarrar lauyan Evans naira dubu ashirin (N20,000)

Evans

Evans ya nemi da a shigar da karar sa kotu yanda dokar kasa ta tsara dan tabbatar da tuhumar da ake masa.

KU KARANTA: Sheriff yayi magana kan hukuncin da kotun koli ta zantar

A wata zantawar, yayi kira da asake shi idan babu wani laifi akansa.

Majiyan news agency of Nigeria(NAN) sun ba da rahoto game da rashin sauraran karan a ranar Alhamis saboda rashin halarta Ogungbeje zuwa kotu.

A ranar saurara karar lauyan evans ya turo wa kotu wsika da bai sai samu halartar zaman ba, yana neman alfarman kotu da ta daga karar zuwa wani lokaci.

Mr Steven Abunike wanda aka turo da wasikan, yayi kokarin mika wa lauyan yan sanda takardan shaidan Rashin yiwuwan halarta baban lauyan, amma yaki sauraran sa.

Lauyan yan sanda ya nuna rashin amincewan sa da wasikan rashin halarta lauyan Evans akan rattaba hanun wani lauyan akan wasikan. Haka ya nuna rashin daukan aikin sa da mahimmanci. Yayi kira da kotu da ta ci su tarar N100,000.

Alkalin yace wasikan da Ogungbeje ya rubuta ya saba kai’da, saboda rashin tura wa lauyan yan sanda kwafin wasikan.

Alkalin ya ja kunnan Ogungbeje akan laifin daya aikata, Cewan ya sabawa irin aikinsu, ya kuma ci shi tarara naira N20,000.

Anka ya dakatad da zaman zuwa 20 ga watan yuli domin sauraron karar.

A karar da Evans ya shigar mai lamba, FHC/L/CS/1012/2017, tsare shi da akayi ba tareda shigar da shi kotu ko kuma bayarda belin shi ya sabawa yancin shi na dan kasa .

A littafin doka mai sakin layin rantsuwa na 27 akan goyon bayan zantawan Baban wanda ake tuhuma (Evans), yace ana cin zarafin yaronsa wajen zartarda shari’a a kafafen yada labarai ba tareda tuhumar kotu ba.

Baban ya kara da cewa, tun kamunda yan sanda suka yiwa dansa, an hana yan uwansa da iyalensa ganin shi amma anbar yan jarida sun gana dashi.

Bugu da kari, Baban Evans yana neman diyyar naira N300m wajen hukuma saboda batancin da aka musu.

Wata Rahoton na Naij.com, ta rawaito cewa shahararen billoniya mai garkuwa da mutane Chukwudumeme uwuamadike wanda aka fi sani da ( Evans) ya maka kai shugaban yan sanda Ibrahim Idris dawasu mutane uku cikin kotu tarayya akan rike shi ba bisa ka’ida ba.

Tare da wa’yanda ya shigar da su kotu harda hukumar yansandar kasa, kwamishinan yan sanda na jihar Legas, special anti robbery squad,hukumar yansanda na jihar Legas.

A wani kara da lauyansa mazaunin jihar Legas Olukoya Ogungbeje ya shigar akan kare hakkin shi na dan kasa. Yace Evans ya na roko da a shigar da kararsa kotu dan tabbatar da laifinsa yadda takardar dokan kasa shafin 35(1)(c)(3)(4)(5)(a)(b) da 36 wacce tayi daidai da Kundin Tsarin Mulkin Najeri na shekara 1999

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel