Wasu sojin Najeriya sun kai kukan su ga Osinbajo

Wasu sojin Najeriya sun kai kukan su ga Osinbajo

- Wasu sojin Najeriya sun kai kukan su zuwa ga Osinbajo

- Sojin sun bayyana cewa kage a kayi masu

- Sojin sun rokon a duba lamarin su

Wasu sojin Najeriya da aka sallama daga aiki a watan Yunin shekarar da ta gabata ne, suka mika sabon korafin zuwa ga mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, su ne cewa wai hukumar sojin Najeriya ba su yi masu adalci ba kuma an nuna masu wariya.

Wannan sabon korafin ya zo ne bayan shekara guda da yin tsoron korafin nasu zuwa ga shugaban kasa Buhari.

A shekarar da ta gabata ne, hukumar sojin kasa ta Najeriya ta sallami wasu sojin nata guda 38 daga aiki, bisa ga zargen aikata laifuka a lokacin zaben kasa na shekarar 2015 da kuma wasu laifuka a kan kudin makamai da aka nema aka nema aka rasa.

Osinbajo: Wasu sojin Najeriya sun kai kukan su

Osinbajo: Wasu sojin Najeriya sun kai kukan su

Binciken PREMIUM TIMES ya nuna cewa, wadansu daga cikin wanda aka sallama daga aikin, wanda ya hadar da wani kwarenren soja day a shahara da kwazo akan aikin na sa, an sallame su ne babu ko wani tallafi ko diyya da aka biya su wanda yana cikin dokokin hukumar sojin.

A lokacin sun yi korafin zuwa ga shugaba Buhari, wanda shekara guda kenan amma sun ji shiru, saboda haka suke tantamar shugaban ma’aikata na soji Gabriel Olanisakin a kan cewa bai isar da sakon sub a zuwa ga shugaban kasa, wanda a yanzu haka daya daga cikin wanda abin ya shafa Ojebo Baba-Ochankpa ya ce ga garinku nan a watan Janairu na shekarar nan.

Mr. Olanisakin wanda shi yake da hurumin mika wannan rubataccen korafin nasu zuwa ga shugaban kasa, ya yi watsi da maganar kotu wadda tace ya tabbatar mata da shaidar cewa ya mika korafin zuwa ga shugaban kasa, don ya yi tafiyar shi kasar waje ganin likita.

A sabon korafin da wadannan sojin 38 da abin ya shafa, karkashin wakilcin Abdul Muhammad, suna rokon da a duba lamarin nasu, kuma sun ce abun kage aka yi musu. Kuma sun bayyana cewa ministan tsaro, shugaban ma’aikata na soji da kuma shugaban ma’aikata na sojin kasa sun taka sawun barawo ne.

KU KARANTA: Wani dan sanda ya harbe kan shi

Shafin PREMIUM TIMES sun ruwaito wasu daga cikin sabon rubataccen korafin nasu da cewa “ laifin da ake zargen su da aikatawa ba wani abu bane face kage da musanya sunayen su da wadanda ainihin suka aikata laifukan”

“Ba a bi tsarin da ya dace na sallama ba, kuma babu wata shaida da aka tabbatar musu da ita da take nuna cewa sun aikata wannan laifuka”. Sun kara da cewa “Sai bayan watanni shidda da sallamar su daga aiki sannan aka kawo sakamakon cewa an rasa gano inda kudin makamai suka shiga”.

A karshe suke cewa, da kuma rubuta kwanan wata kamar haka 6/Yuli/2017, suna rokon gwamnatin tarrayya ta Najeriya da ta duba wannan korafin nasu kuma ta tsananta bincike a kan wannan al’amari domin a gano ainihin wadanda suka aikata wannan laifukan.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel