Wasu abokai 4 sun yiwa wata daliba fyade (hoto)

Wasu abokai 4 sun yiwa wata daliba fyade (hoto)

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun sanar da kamun wasu dalibai hudu na makarantar kwalejin Adeyemi College of Education (ACE) dake jihar Ondo, bayan sun yi ma wata yarinya fyade.

An bayyana sunayen masu laifin a matsayin Olakunle Adetuyi, Timilehin Akinola, Tobi Olagbaju da kuma Adebisi Adeyemi, dukka shekarun sun bai haura 24 zuwa 26 ba. Zuwa yanzu jami’an yan sandan na neman cikon dayansu wanda suka aikata ta’asar tare wato Eric Nwage,

Ita wacce aka yi wa fyaden dalibar koyon Tarihi da Turanci ce ‘yar shekara 22 sannan kuma budurwan daya daga cikin wadanda suka aikata laifin ne Timilehin Akinola.

A lokacin da ake gabatar da masu laifin ga manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan jihar a garin Akure, babban birnin jihar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ondo, Hilda Ibifuro-Harrison, ta bayyana cewa wadanda ake zargin su yaudare yarinyar ne zuwa gidan Olagbaju dalibin makaranta Rufus Giwa Polytechnic Owo ne sannan kuma abokin Timilehin.

Wasu abokai 4 sun yiwa wata daliba fyade (hoto)

Wasu abokai 4 sun yiwa wata daliba fyade Hoto: Alummata

A yayin da dalibar ta isa gidan Olagbaju gida mai lamba 17 a Funbi Fagun Housing Estate a birnin Ondo, a nan ne suka samu nasaran yi mata fyaden.

KU KARANTA KUMA: Caraf an fara kame masu kazamin lodi a manyan titunan TarayyaCaraf an fara kame masu kazamin lodi a manyan titunan Tarayya

Daya daga cikin abokiyan wadda aka yi ma fyaden ne ta kai kara wurin jami’an tsaro masu zaman kan su, wadanda su suka kama wadanda suka aikata laifin bayan sun gudunar da binciken suka mika su hannun ‘yan sanda domin a hukunta su kamar yadda doka ta tsara.

“Daya daga cikin wadanda ake zargi, Olakunlle ya dauke bidiyon su a yayin da suke aikata wannan mummunan aikin’

inda a ciki bidiyon suka fada mata cewa za su mata asiri idan har ta kai su kara”

“A lokacin da ‘yan sanda ke gudunar da binciken su, sun gano wayar da layar da suke gaya mata cewa za su mata asiri da shi”

Kwamishan ta kuma kara da cewa, yarin wadda aka wa fyaden na asibiti ana mata magani a asibitin Ile Ife, a jihar Osun.

A lokacin da ya ke furta wa bayan ya amince da aikata wannan laifin mista Akinola ya bayyana cewa shi da abokan sa sun yiwa yarin fyade.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel