Dan ƙwallo ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa har lahira (HOTUNA)

Dan ƙwallo ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa har lahira (HOTUNA)

- Wani dan kwallo dan kasar Ghana Nyatakyi Solomon ya hallaka mahaifiyarsa

- Ya hallaka kanwarsa da mahaifiyarsa ta hanyar caccaka musu wuka

Wani dan kwallo dan kasar Ghana Nyatakyi Solomon ya hallaka kanwarsa da mahaifiyarsa a gidansu dake garin Parma ta kasar Italiya ta hanyar caccaka musu wuka.

Jami’an Yansandan Parma sun samu nasarar kama Solomon wanda ke harkar buga kwallo a kungiyar Parma, Solomon ya shiga hannun Yansanda ne jim kadan bayan ya fito daga filin atisaye na Milan.

KU KARANTA: Rundunar Sojin sama da sabunta wasu jiragen leken asiri masu sarrafa kansu (HOTUNA)

Ana zargin Solomon da caccaka ma mahaifiyar tasa tare da kanwarsa wuka ne a jikkunansu a wurare da dama, daga bisani kuma ya amsa laifinsa, inda yace lallai shi ya kashe mamatan a gidansu bayan mahaifinsa da kannensa sun fita.

Dan ƙwallo ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa har lahira (HOTUNA)

Gawar mahaifiyar

NAIJ.com ta ruwaito kanin Solomon, Raymond ne ya gano gawar mahaifiyar tasu dana kanwar tasu bayan dawowarsa daga wajen aiki.

Dan ƙwallo ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa har lahira (HOTUNA)

Dan ƙwallon da gawar mahaifiyarsa

Dan ƙwallo ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa har lahira (HOTUNA)

Makwabta suna jimami

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda yan kungiyar asiri ke kashe matasa a Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel