Wata mata ta rasa ran ta a sakamakon tashin jirgi a New Zealand

Wata mata ta rasa ran ta a sakamakon tashin jirgi a New Zealand

- Iskar tashin Jirgi ta kashe wata mata

- Mutane na zuwa bakin teku shan iska

- Tazara ce kadan tsakanin filin jirgin da bakin Teku

Wata mata a kasar New Zealand ta rasa ran ta a sakamakon iskar jirgin sama yayin da yake tashi.

Matar mai shekara 57, tana rike da katangar filin jirgin ne yayin da jirgin zai tashi. Duk da alamomin tsaron da aka rubuta na mutane suyi baya-baya da hattara daga jikin katangar filin jirgin, 'yan Sanda suka bayyana.

Wata mata ta rasa ran ta a sakamakon tashin Jirgi a New Zeland

Wata mata ta rasa ran ta a sakamakon tashin Jirgi a New Zeland

Filin Jirgin saman mai suna Princess Juliana bashi da nisa daga bakin tekun Sint Maarten a garin Karibiya. Duk sa’adda jirgi zai tashi ko sauka ana iya ganin shi kasa-kasa.

Hakan ne yasa duk sa’adda jirgi zai tashi, mutanen da ke zuwa bakin tekun yawon bude ido da shan iska suna iya takawa zuwa bakin katangar filin jirgin don ganin tashi da saukar jirgi.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Kwadago na kashedi ga APC kan batun karin albashi

Karfin iskar tashin jirgin ne ya jawo matar ta fadi kasa, har taji mummunan rauni. An yi gaggawar kai ta asibiti amma daga baya rai yayi halin sa.

Tashi da saukar Jirgi a filin na garin sanannen abu ne mai jawo hankalin masu yawon shakatawa sosai a fadin Duniya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel