Rashin lafiya: Dole Shugaba Buhari ya koma Daura-Inji Adeyanju Deji

Rashin lafiya: Dole Shugaba Buhari ya koma Daura-Inji Adeyanju Deji

- Wani fitaccen Matashi a Jam'iyyar adawa ya soki Shugaban kasa Buhari

- Dole Shugaba Buhari ya ajiye mulki idan ba za a san abin da ke damun sa ba

- Har yau babu wanda ya san abin da ke damun Shugaban kasar

Wani Matashi mai suna Adeyanju Deji da ke cikin manya a Jam'iyyar adawa ya soki Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da halin rashin lafiyar sa.

Rashin lafiya: Dole Shugaba Buhari ya koma Daura-Inji Adeyanju Deji

Wani Matashin 'Dan PDP Adeyanju Deji

Adeyanju Deji yace ya zama dole Muhammadu Buhari yayi wa 'Yan Najeriya halin da yake ciki don kuwa shi ne Shugaban kasa kuma da dukiyar kasa ake kula da rashin lafiyar na sa da ba a san menene ba.

KU KARANTA : Rasuwar Akande: Shugaba Buhari ya kira gida

Rashin lafiya: Dole Shugaba Buhari ya koma Daura-Inji Adeyanju Deji

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Rikakken Dan PDP Deji yace idan har ana so 'Yan Najeriya su daina tambayar halin da Shugaban na su yake ciki to sai Muhammadu Buhari yayi murabus ya koma Garin Daura salin-alin kowa ya huta.

Kun ji cewa Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda su kayi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Landan inda su ka hadu shekaran jiya da dare.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Fafutukar Biyafara zuwa yanzu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel