‘Yan Najeriya na farin ciki da ganin cewa PDP ta kusa ture APC – Fani-Kayode

‘Yan Najeriya na farin ciki da ganin cewa PDP ta kusa ture APC – Fani-Kayode

- Mista Fani-Kayode ya nuna farin ciki da hukunci kotun koli game da PDP

- Ya ce jam’iyyar adawa a shirye take ta kwace gwamnati

- Ya yi ikirarin cewa ‘yan Najeriya sun gaji da gwamnatin Buhari

Femi Fani-Kayode ya nuna farin ciki kan nasarar bangaren Ahmed Makarfi na jam’iyyar PDP a kotun koli, cewa alamu ne dake nuni ga tashin jam’iyyar.

Kungiyar masu sharia biyar ne suka yi watsi da Sanata Ali Modu Sheriff sannan kuma suna tabbatar da Makarfi a matsayin ainahin shugaban jam’iyyar a hukunci da suka yanke a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.

Da ya fito a shirin Politic Today a Channels television, Fani-Kayode cewa hukuncin kotun koli ya kasance nasara ga damokradiya.

Dan jamiyyar na PDP ya ce miliyoyin ‘yan Najeriya na farin ciki kamar yadda hakan ke nufin za’a kayar da jam’iyyar adawa ta APC nan ba da jimawa ba.

KU KARANTA KUMA: Caraf an fara kame masu kazamin lodi a manyan titunan Tarayya

Fani-Kayode ya bayyana cewa ‘yan Najeriya zasu sake gigin imani da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa kotun koli ta kaddamar da kungiyar Makarfi a matsayin ainahin shugaban jam’iyyar PDP bayan an sha gwagwarmaa tsakanin bangaren sa da na Ali Modu Sheriff.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel