Zumudi kan Biafra: Nnamdi Kanu bai isa ya hana zabe a garuruwan Ibo ba, Inji Orji Kalu

Zumudi kan Biafra: Nnamdi Kanu bai isa ya hana zabe a garuruwan Ibo ba, Inji Orji Kalu

- Nnamdi Kanu bai isa ya hana zabe a garuruwan Ibo ba – Inji Orji Kalu

- Bai dace Kanu ya hana mutane kada kuri'a ba

- Bana goyon bayan Kanu amma kundin tsarin mulki ta bashi damar fadin ra'ayinsa

- Kanu yana da ikon neman kafa kasar Biafra amma ba tare da karya doka ba.

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzo Kalu yace shugaban kungiyar IPOB masu kokarin kafa kasar Biafra bai da ikon da zai hana zabe a garuruwan ibo har sai gwamnatin tarayya ta zauna dashi domin tattauna wa.

Tsohon gwamnan kuma jigo a jami’iyyar APC, a yayin da yake Magana a Jihar Abia yace, Umarni da Nnamdi Kanu ya baiwa mabiyansa na guje ma zaben ya saba ma dokan kasa.

Zumudi kan Biafra: Nnamdi Kanu bai isa ya hana zabe a garuruwan Ibo ba – Inji Orji Kalu

Zumudi kan Biafra: Nnamdi Kanu bai isa ya hana zabe a garuruwan Ibo ba – Inji Orji Kalu

Ya amince Kanu yana da daman ya nemi kafa kasar Biafra amma bashi da ikon ya hana mutane kada kuri’ar su idan zabe ya zo.

Ya ce: “Bai dace kungiyar IPOB tayi irin wannan kiran ba, ya saba ma dokar kasa. Suna da damar gwagwarmayar neman kafa kasar su amma basu da ikon hana wasu mutanen zaben shugabanin su.

“IPOB suna da ikon fadan ra’ayinsu, tunda kundin tsarin mulki ya ba kowane dan kasa ikon fadin albarkacin bakinsa, amma ba daidai bane a karya doka wajen yin hakan.

“Na je kurkuku duba Kanu a lokacin yana kulle, nayi Magana dashi kuma naje wurin iyayensa a garin Afara Ukwu kuma suma nayi Magana da su."

DUBA WANNAN: Kungiyar kwadago na kashedi kan karin albashin da APC tayi alkawari

Wannan bai nuna cewa ina goyon bayan sa ba kamar yadda wasu suke tsamani, amma duk da haka bana adawa dashi. Yana da daman ya nemi kafa kasar tasu sai dai ya kamata yabi hanyoyin da doka ta amince dasu."

"Babu wata babbar Kasa a duniya da ke goyon bayan raba Najeriya, ina fatan masu neman raba kasar zasu lura da hakan".

"Abin da nake ganin yafi dacewa shine mu hada kan mu waje daya mu nemi hakin mu na shugabancin kasan nan, mu nemi ayi mana adalci da rashin nuna fifiko a tsakanin banagarorin Najeriya; wadannan sune abubuwan da nake ganin ya dace mu nema."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel