YANZU YANZU: ‘Yan majalisar wakilai na PDP sun ba Buhari wa’adin barin mulki

YANZU YANZU: ‘Yan majalisar wakilai na PDP sun ba Buhari wa’adin barin mulki

- Mambobin majalisar wakilai sashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sun kaddamar da cewa akwai gurbi a Aso Rock

- Sun bayyana hakan ne bayan nasarar kawo karshen rikicin PDP da kotu tayi

- Jam'iyyar ta ce gwamnatin APC ta gaza cika alkawaran da ta dauka sai ma talautar da 'yan Najeriya da tayi da kuma rashin basu tsaro

A safiyar yau Alhamis, 13 ga watan Yuli, mambobin majalisar wakilai sashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sun kaddamar da cewa akwai gurbi a Aso Rock a shekarar 2019

Dan majalisa Leo Okuweh Ogor, jagoran jam’iyyar adawa na majalisar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai bayan nasarar kawo karshen rikicin jam’iyyar da kotu t yi.

Da yake magana a madadin majalisar, Ogor ya fada wa manema labarai cewa gwamnatin APC na ta daukan alkawara ba tare da aiki ba, sai ma talautar da ‘yan Najeriya wanda ke fama da yunwa da rashin tsaro a yanzu.

KU KARANTA KUMA: Caraf an fara kame masu kazamin lodi a manyan titunan Tarayya

Ya ce tunda APC ta gaza gurin inganta al’amarin kasar fiye da yadda ta same ta, ya kamata ta ga nasarar PDP a kotu a matsayin wa’adin barin mulki a 2019.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel