Wani dan sanda ya harbe kan shi

Wani dan sanda ya harbe kan shi

Rahotanni sun kawo cewa wani jami’in dan sanda a kasar Ghana mai suna, Ebenezer Kofi Okyere, wanda ke aiki a Central Police Station a Kumasi da ke yankin Ashanti a kasan Ghana ya kashe kansa.

Wani mai amfani da shafin Facebook Isaac Badiako Justice ne ya buga labarin a shafin sa. A cewar sa makwabtan dan sandan sun ji sautin karar bindiga, koda suka isa dakin nasa sun isar da gawarsa a kwance.

Bisa ga rahoto jami’in dan sandan ya kashe kansa ne bayan y agama amsa kiran da akayi masa a waya bayan an zarge shi da zama uban wani jariri da aka haifa.

A cewar budurwar dan sandan, ta ji yana ce ma mutin da suke waya zai kashe kansa idan harka aka dage kan cewa shine mahaifin yaron.

KU KARANTA KUMA: Caraf an fara kame masu kazamin lodi a manyan titunan TarayyaCaraf an fara kame masu kazamin lodi a manyan titunan Tarayya

Da gama wayar ta sa kawai sai ya fadawa budurwarsa ta bar dakin kafin ya harbi kan sa a makogwaro.

A firgice makwabtan sa suka shiga dakin shi suka tsinnce gawan shi a kan kujera. A yanzu haka gawarsa na asibiti.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel