Fashi da makami: An kama mutum 13 a jihar Kano

Fashi da makami: An kama mutum 13 a jihar Kano

- Fashi da makami ya zama ruwan dare

- An kama wasu 'yan fashi da makami a jihar Kano

-'Yan sanda sun ce za su cigaba da bakin kokarin su

A jiya laraba 12 ga watan Yuli, wasu jami'an tsaro na 'yan sanda suka yi nasarar cafke wasu 'yan fashi da makami a jihar Kano.

Kakakin 'yan sandan, DSP Magaji Musa Majia, ya bayyanawa manema labarai cewa sunyi nasarar cafke wasu mutum 2 da ake zargin 'yan fashi da makami ne , Yusuf Umar mai shekaru 30 dan kauyen Tokarawa da Amadu Mohammed mai shekaru 33 dan kauyen Kankan, duk su biyun 'yan karamar hukumar Gezawa ne, kuma an yi nasarar cafke su din ne a Tokarawa a lokacin da suke kan aikin nasu na fashi.

Jami'in yace sun kama makamai daban daban, kayan sanyawa na dakaru, babura biyu, da kuma mota kirar Golf me lamba AX571KMC wadda aka yi mata fenti irin na tasi. 'Yan fashin sun tabbatar musu da cewa kungiya ce da su ta mutum shidda.

Haka kuma, jami'an tsaron sun yi nasarar cafke wasu mutum shidda wanda su ma ake zargin su da kwacen motoci da babura, kuma an kama su ne da mota kirar Golf da babura guda uku.

Fashi da makami: An kama mutum 13 a jihar Kano

Fashi da makami: An kama mutum 13 a jihar Kano

Majiya cigaba da bayanin cewa sun kama wasu 'yan fashin suma, wanda su ka yi kwacen wata mota kirar Sienna a ranar 29 ga watan Yuni na shekarar nan, kuma sun kama su ne da wannan mota da kuma wata motar kirar Golf III a tare dasu, wadda a yanzu haka an mayar wa da mai Sienna motar shi.

KU KARANTA: Ziyarar Osinbajo ga Buhari yaudara ce - Fayose

Ya kara da cewa, jami'an sun yi nasarar kama wani Yahaya Usman a unguwar Malali ta jihar Kaduna, wanda ya shahara da satar motoci, kuma an kama shi ne da wata kirar Honda Civic me bakin fenti.

Majia ya tabbatar wa da manema labarai cewa, za su cigaba da iyaka bakin kokarin su don ganin cewa duk wani dan ta'adda, fashi da makami da satar kayan jama'a yazo hannu.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel