Wani gidan rediyo ya maka Gwamnatin Tanko Al-Makura a Kotu

Wani gidan rediyo ya maka Gwamnatin Tanko Al-Makura a Kotu

- Wani gidan rediyo ya maka Gwamnatin Tanko Al-Makura a Kotu

- Gidan rediyon na bukatar a biya ta Naira Biliyan daya da rabi

- Gwamnatin Jihar ta rusa gidan rediyon can kwanakin baya

Mun samu labari cewa an maka Gwamnatin Jihar Nasarawa a Kotu a dalilin rusa wani gidan rediyo da tayi kwanakin baya.

Wani gidan rediyo ya maka Gwamnatin Tanko Al-Makura a Kotu

Gwamnatin Tanko Al-Makura ta shiga uku?

Gidan rediyon na 'Breeze FM' da ke kan lamba 99.9 ta kai karar Gwamnatin a wani babban Kotun da ke babban Birnin Jihar na Lafiya inda ake neman a biya ta Naira Biliyan daya da rabi na barna da aka yi mata.

KU KARANTA: Wata Jarida ta soki Gwamnatin Buhari

Gidan rediyon wanda na 'yan kasuwa ne ta kuma nemi a tursasawa Gwamnatin Jihar ta ba da hakuri sannan kuma ta guji kara taba wani sashe na gidan rediyon don kuwa tun farko ba a bi doka ba wajen rusa gidan ba.

Kwanaki mai girma Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura yayi kira a soke daya daga cikin Majalisun Tarayya don kuwa babu dalilin a cigaba da aiki da dukka biyu ba Inji Gwamnan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da Rikicin Taurari Wiz kid da Davido

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel