Rakiyar Kura: Sojoji sun fatattaki mayaƙan Boko Haram har yankin tafkin Chadi (HOTUNA)

Rakiyar Kura: Sojoji sun fatattaki mayaƙan Boko Haram har yankin tafkin Chadi (HOTUNA)

- Jami'an rundunar Soji ta fatattaki yan Boko Haram har tafkin Chadi

- Sojoji sun salwantar da rayuwan yan Boko Haram guda 4 yayin rakiyar

A cigaba da kokarin ta kakkabe yankin Arewa maso gabas daga ayyukan yan ta’addan Boko Haram, rundunar Soji dake karkashin Birget ta 7 tayi dauki ba dadi da yan Boko Haram a kauyen Dawashi.

Kaakakin rundunar Sojin kasa, Birgediya SK Usman ya bayyana anyi wannan musayar wuta ne tsakanin Sojojin da mayakan Boko Haram a kauyen Dawashi dake kan iyakar Najeriya da yankunan tafkin Chadi.

KU KARANTA: Karshen rikicin PDP: Jonathan yayi murna da fatattakar Sheriff daga muƙamin shugaba

Sakamakon karan battan, Sojoji sun samu nasarar hallaka yan Boko Haram su 4 tare da jikkata da dama, inda sauran suka ce ‘kafa mai naci ban baki ba’ suka bar baburansu da wasu makamansu a wajen.

Rakiyar Kura: Sojoji sun fatattaki mayaƙan Boko Haram har yankin tafkin Chadi (HOTUNA)

Kayayyakin da aka kwato a hannun mayaƙan Boko Haram

NAIJ.com ta ruwaito Birgediya SK na bayyana cewa tuni Sojoji suka banka ma baburan yan ta’addan wuta, domin hana su amfani dasu wajen aikata ayyukan ta’addanci akan jama’an da basu ji ba, basu gani ba.

Rakiyar Kura: Sojoji sun fatattaki mayaƙan Boko Haram har yankin tafkin Chadi (HOTUNA)

Sojoji suna kona kayayyakin

Haka zalika, rundunar Sojin bataliya ta 145 ta kakkabe yan Boko Haram daga garuruwan Gashigar, Asaga, Bukarti da sauran kauyuka makwabta, a yayin wannan shara, Sojoji sun kashe yan ta’adda 2, sun kama 2 tare da kwato makamai, alburudai da babura 4.

Rakiyar Kura: Sojoji sun fatattaki mayaƙan Boko Haram har yankin tafkin Chadi (HOTUNA)

Sojoji sun kona mafakan Boko Haram

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda Sojoji ke yi ma Boko Haram luguden wuta:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel