Matasan Ijaw sunyi barazanar mamaye majalisar dokoki kan zagin Jonathan

Matasan Ijaw sunyi barazanar mamaye majalisar dokoki kan zagin Jonathan

- Matasan Ijaw sun yi barazanar mamaye majalisar dokoki bisa zargin zagin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Matasan sun yi gargadin cewa idan majalisar dokoki ta nace kan cewa sai Jonathan ya gurfana a gaban ta, zasu mamaye majalisar

- Sun ce ya zama lallai abi ka’ida idan za’a gayyaci tsohon shugaban kasar saboda ba mutumin kawai bane a kasar

Matasan Ijaw sun yi barazanar mamaye majalisar dokoki bisa zargin cewa ‘yan majalisa na tozarta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta wata sanarwa daga shugaban ta, Oweilaemi Perestubor a Asaba, jihar Delta, jaridar Guardian ta rahoto.

Matasan sun yi gargadin cewa idan majalisar dokoki ta nace kan cewa sai Jonathan ya gurfana a gaban ta, zasu mamaye majalisar.

Matasan Ijaw sunyi barazanar mamaye majalisar dokoki kan zagin Jonathan

Matasan Ijaw sunyi barazanar mamaye majalisar dokoki kan zagin Jonathan

A cewar kungiyar ya zama lallai abi ka’ida idan za’a gayyaci tsohon shugaban kasar saboda ba mutumin kawai bane a kasar.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC tayi ram da wani Bawan Allah a KadunaHukumar EFCC tayi ram da wani Bawan Allah a Kaduna

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Patience Jonathan ta nemi doki kan abun da ta bayyana a matsayin muzgunawa daga hukumar EFCC da Ibrahim Magu ke jagoranta a kanta da mambobin gidanta.

Matar tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan, tayi ikirarin cewa Magu ya rubuta wasika ga hukumar kasar turai inda ya bukaci su hana ta biza.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel