Ziyarar Osinbajo ga Buhari yaudara ne – Fayose

Ziyarar Osinbajo ga Buhari yaudara ne – Fayose

- Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya ce ‘yan Najeriya na bukatar bidiyon shugaban kasa Buhari yayinda yake jawabi a gare su

- Gwamnan ya kalubalanci na kewaye da Buhari da su tabbatar ma ‘yan Najeriya da cewan shugaban kasar na cikin koshin lafiya ta hanyar bayyana ma jama’a shi

- Fayose ya ce Buhari ya yi Magana ga ‘yan Najeriya a bayyane don tabbatar da cewa zai iya ci gaba a matsayin shugaban kasa

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana rahoton ziyarar da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai ma shugaba Muhammadu Buhari a Landan a matsayin makircin jamíyyar APC don su boye ainahin halin da shugaban kasar ke ciki.

Gwamnan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli daga mataimakin sa a kafofin watsa labarai, Lere Olayinka, ya nace kan cewa abunda ‘yan Najeriya ke bukata don kore kokwanton su game da lafiyar shugaban kasa shine bidiyon shugaba Buhari inda zaiyi jawabi a gare su ba wai wani ziyara ba wanda ba’a nuna ma jama’a hoto ko bidiyo ba.

Fayose ya kalubalanci na kewaye da Buhari da su tabbatar ma ‘yan Najeriya da cewan shugaban kasar na cikin koshin lafiya ta hanyar bayyana ma jama’a shi.

Ziyarar Osinbajo ga Buhari yaudara ne – Fayose

Ziyarar Osinbajo ga Buhari yaudara ne inji Fayose

Fayose ya kuma yi barazanar bayyana sabbabin hotuna 11 na shugaban kasar domin tabbatar da cewa Buhari na cikin mawuyacin hali.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan - Fayose2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan - Fayose

Gwamnan ya ce zai saki hotuna 11 idan wadanda ke kan mulki suka ci gaba da yaudarar yan Najeriya game da gaskiyar halin da shugaban kasar ke ciki.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel