An bayyana cikakken bayani a kan ganawar Osinbajo da shugaba Buhari

An bayyana cikakken bayani a kan ganawar Osinbajo da shugaba Buhari

- Farfesa Osinbajo ya samu yarda daga shugaba Muhammadu Buhari gurin yanke wasu muhimman shawara

- Wannan na daga cikin abunda suka tattauna a lokacin ziyarar sag a shugaban kasa a birnin Landan

- Wasu ministoci na iya rasa kujerar su a cewar majiyoyi

Cikakkun bayanai sun fara billowa na ganawar mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan inda aka mayar da hankali a kan ministoci.

Mukaddashin shugaban kasar ya tashi zuwa birnin Landan a ranar Talata, 11 ga watan Yuli don ganawa da shugaban kasa sannan kuma a cewar jaridar The Nation, sun mayar da hankali ne a kan ci gaban kasar musamman yayinda abun ya shafi majalisar.

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa wacce tayi Magana a kan sharadin baza’a bayyanata ba, tace ba zai yiwu a shafe dukkanin majalisar ba “saboda kasar bazata iya hakan ba a yanzu”. Amma dai ana iya sake wasu ministoci.

An bayyana cikakken bayani a kan ganawar Osinbajo da shugaba Buhari

An bayyana cikakken bayani a kan ganawar Osinbajo da shugaba Buhari

An kuma tattaro cewa Osinbajo ya samu yarda kan wasu nade-nade da kuma yanke muhimman shawara.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan - Fayose

Wani mamba na majalisar yace Osinbajo ya basu bayani game da lafiyar Buhari.

"Mukaddashin shugaban kasa ya fada mana cewa babu wani abun tashin hankali. Y ace shugaban kasar na murmurewa sosai.

“Dukkanmu mun samu kwanciyar hankali saboda wannan bayani ya fito daga hannu mafi inganci da muka samu."

A halin yanzu, Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana rahoton ziyarar da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai ma shugaba Muhammadu Buhari a Landan a matsayin makircin jamíyyar APC don su boye ainahin halin da shugaban kasar ke ciki.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel