Yan ƙunar baƙin wake sun kashe yan ƙato da gora tare da ýan zaman Makoki

Yan ƙunar baƙin wake sun kashe yan ƙato da gora tare da ýan zaman Makoki

- Yan kunar bakin wake sun kai hari ga masu zaman Makoki

- Boko Haram ta kai hare hare daban daban a jihar Maiduguri a ranar Talata

Yayan kungiyar Boko Haram sun kashe sama da mutane 19 a hare hare daban daban da suka kai babban birnin jihar Borno, Maiduguri a ranar Talata 11 ga watan Yulio.

Wannan mummunan hari ya faru ne yayin da wasu jama’a ke zaman makoki sun karbar gasiwuar rasuwar wani dan uwansu, a lokacin da yar kunar bakin waken tayi kansu, kamar yadda BBC Hausa ta rwuaito

KU KARANTA: Anyi musayar wuta tsakanin yan fashi da Yan sanda a titin Zaria-Kano, an kashe 2

Haka zalika wata budurwa ta kai harin bakin wake a shingen yan kato da gora masu taimaka ma jami’an tsaro a cikin garin Maiduguri domin sanya idanu kan masu shige da fice ciki da wajen garin, inda ta hallaka matasan su 3.

Yan ƙunar baƙin wake sun kashe yan ƙato da gora tare da ýan zaman Makoki

Jana'iza

Sai kuma hari na uku, inda yar kunar bakin waken ta afka ma matasan Sibilyan JTF dake shan shayi a wata majalisar shan shayi, indomie da kwai.

Yan ƙunar baƙin wake sun kashe yan ƙato da gora tare da ýan zaman Makoki

Harin ƙunar baƙin wake

Dayake tabbatar da hare haren, NAIJ.com ta ruwaito kwamishinan yansandan jihar Borno, Damian Chukwu yace yawancin wadanda suka hallaka jami’an kato da gora ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli barnar da Boko Haram tayi a Maiduguri:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel