Buhari ya kira, sannan ya rubuta wasika ga Akande kan mutuwar matarsa

Buhari ya kira, sannan ya rubuta wasika ga Akande kan mutuwar matarsa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi rubutu da kuma kiran shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Cif Bisi Akande

- Ya kira ne domin yi masa taáziyar rashin matarsa, Omowunmi

- Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana hakan ga mane labarai

A ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, fadar shugaban kasar tace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi rubutu da kuma kiran shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Cif Bisi Akande, kan waya don yi masa ta’aziya kan mutuwar matarsa, Omowunmi.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kafofin watsa labarai, Garba Shehu, ya bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labarai a Abuja.

Shehu ya bayyana cewa shugaban kasar ya nuna bakin cikin sa kan mutuwar matar Akande na shekaru 50.

Buhari ya kira, sannan ya rubuta wasika ga Akande kan mutuwar matarsa

Buhari ya kira, sannan ya rubuta wasika ga Akande kan mutuwar matarsa

Ga sakon shugabna kasar kamar haka: “Na samu labarin nab akin ciki na rasuwar matarka, Madam Omowunmi Akande a safiyar nan. Ina bibiyar kiran wayarmu da wannan wasikar na ta’aziya, wanda ke zuwa daga zuciya na.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan - Fayose2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan - Fayose

“Rashin mata wanda aka dauki tsawon shekaru 50, cikin so da kauna duk runtsi duk wuya ana tare, babban gibi ne ga mutun. Dan Allah ka isar da ta’aziya na ga ahalin gidan Akande da kuma ‘yan uwa da abokan arziki bisa wannan babban rashi.

“Allah ya baka juriya da imani kan rashin ta.”

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel