Karshen rikicin PDP: Jonathan yayi murna da fatattakar Sheriff daga muƙamin shugaba

Karshen rikicin PDP: Jonathan yayi murna da fatattakar Sheriff daga muƙamin shugaba

- Tsohon shugaban kasa Jonathan yayi murna da nasarar Makarfi

- Goodluck Jonathan ya shawarci Sheriff yazo a gina jam'iyyar PDP

Goodluck Jonathan ya bayyana murnarsa da faduwar sanata Sheriff a kotun koli tare da samun nasarar sanata Makarfi a kotun, yayin da alkalan kotun kolin suka yanke hukuncin Makarfi ne halastaccen shugaban jam’iyyar.

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook da Tuwita inda yace “Ina mai matukar farin ciki sakamakon kawo karshen rikicin data dabaibaye jam’iyyar a kotun koli.”

KU KARANTA: Saura ƙiris na auri ɗiyata, saboda tsabar yawan ýaýana – Inji mai ýaýa 100

Jonathan ya kara da cewa wannan hukunci zai yi matukar tasiri ga hadin kan jam’iyyar PDP, sa’annan ya taya bangaren halastaccen shugaban jam’iyyar, Sanata Ahmed Makarfi.

Karshen rikicin PDP: Jonathan yayi murna da fatattakar Sheriff daga muƙamin shugaba

Jonathan

Jonathan yayi kira ga wadanda suka sha kayi dasu dauki dangana, su yi hakuri, sa’annan su yi koyi da tsohon shugaban kasa janar Yakubu Gowon, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Bugu da kari Goodluck ya shawarci tsagin Sheriff da kada su fita daga jam’iyyar, su dawo a rungumi juna a tafiyar da jam’iyyar gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cigaba da aka samu a ilimi a wanan jihar, Kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel