2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan - Fayose

2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan - Fayose

- Fayose yace PDP ce za ta lashe zaben 2019

- Gwamnan ya tabbatar da ana demokuradiya a kasar nan

- Jama’ar Najeriya sun kai makura a kan mulkin APC

A ranar larabar da ta gabata ne gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, wanda dan jam’iyar PDP ne, ya bayyanawa manema labarai cewa “jam’iyar ta su za ta karbi shugabancin kasar nan a shekarar 2019.

2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan inji Fayose

2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan inji Fayose

Fayose wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin jami’iyar PDP ta Najeriya baki daya, ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai bayan kotun kolu ta Najeriya ta tabbatar da Ahmed Makarfi a matsayin shugaban jam’iyar PDP ta kasa baki daya.

Shafin Daily Post sun ruwaito daga bakin kakakin gwamnan jihar Ekiti, Lere Olayinka, cewa “hukuncin da kotun kolu ta zartar a kan tabbatar da Ahmed Makarfi a matsayin shugaban jam’iyar ta su, ya tabbatar mu su da cewa lallai Demokuradiya ta samu wajen zama a kasar nan.

KU KARANTA: An ceto wata mata da aka kulle a daki na tsawon shekara 15

Yace “kuma wannan hukuncin ya nuna alamar cewa PDP za ta dawo shugabancin kasar nan a shekarar 2019, saboda haka shugaba Buhari da ‘yan tawagar sa su fara tattara ina-su-ina-su domin su za su karbi mulki 2019."

Ya kuma kara tabbatarwa da manema labarai cewa jama’ar Najeriya sun gaji da wannan mulkin na kama karya da ake musu, da kuma irin rikon sakainar kasha da a ke yiwa tattalin arzikin kasar nan domin kuwa dalilin haka ne kamfanin sadarwa na Etisalat su ka ce zasu bar Najeriya a makonnin da su ka gabata.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel