Babu wanda zai iya tsige shugaba Buhari daga mulki, wata kungiya tayi gargadi

Babu wanda zai iya tsige shugaba Buhari daga mulki, wata kungiya tayi gargadi

- Ziyarar da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai ma shugaba Muhammadu Buhari kwanann nan a birnin Landan na ci gaba da tattara cece-kuce

- Wata kungiya mai suna Coalition for Sustainable Democracy ta sanya baki a alámarin

- Kungiyar ta yi gargadi cewa duk wani yunkuri da wasu jamián gwamnati keyi na son cire shugaba Buhari ba zai yi tasiri ba

Wata kungiya mai suna Coalition for Sustainable Democracy ta yi gargadi ga jamián gwamnatin tarayya da ake zargi da wani yunkuri na son sauke shugaban kasa Buhari.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Mohammed Yakubu ya aika ma NAIJ.com, kungiyar ta ce wadanda ke shirya makarkashiya domin kwace gwamnati ta kofar baya bazasu yi tasiri ba.

Sun bayyana cewa suna bibiyar komai sannan kuma sun sha alwashin yin duk wani abu da zasu iya don kare tsarin damokradiyya da ake kai a yanzu a kasar.

Babu wanda zai iya tsige shugaba Buhari daga mulki, wata kungiya tayi gargadi

Babu wanda zai iya tsige shugaba Buhari daga mulki, wata kungiya tayi gargadi

Sun nuna jin dadinsu ga ziyarar da Osinbajo ya kai ga shugaba Buhari, sun kara da cewa ci gaba ne mai kyau.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP za ta karbi mulkin kasar nan - Fayose

Kungiyar ta kuma yi gargadin cewa ayyukan wasu mutane dake kusa da Osinbajo zai tada zaune tsaye ne ga zaman lafiya da hadin kan kasarmu fiye da sauran rikicin kabilanci, harma da ýan taáddan Boko Haram.

Sun bayyana cewa wadannan kungiyoyi da mutane ba taimakon mukaddashin shugaban kasa suke yi ba, sun kara da cewa yunkurinsu zai haddasa Karin matsaloli ne a gare shin (Osinbajo).

A halin da ake ciki, shugabannin jamíyyar All Progressives Congress (APC) basu ji dadin Baraka dake tsakanin majalisar dokoki da fadar shugaban kasa ba a yanzu.

Shugabannin jamíyyar sun yanke shawarar sanya baki a cikin alámarin wanda ke barazanar tarwatsa jamíyyar.

Musabbabin rikicin shine tabbatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel