‘Yan Najeriys bazasu ji dadi ba idan APC ta gaza aiki – Nasir El-Rufai

‘Yan Najeriys bazasu ji dadi ba idan APC ta gaza aiki – Nasir El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa cika aiki na da alaka da iya aiki; sannan jam’iyyar APC bata da wani hujja idan ta gaza ta ko wani fanni

- El-Rufai ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun zabi jam’iyyar a shekarar 2015, sannan kuma suna da kyakyawan zato ga gwamnatin

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa domin sanya ‘yan Najeriya cikin farin ciki, ya zama dole jam’iyyar sa ta APC ta yi aiki a ko wani mataki.

A cewar rahotanni, gwamnan yay i furucin sa ne a Arewa House, Kaduna, a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli, yayinda yake magana a wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da aiki.

KU KARANTA KUMA: Caraf an fara kame masu kazamin lodi a manyan titunan Tarayya

A halin yanzu, NAIJ.com ta rahoto a baya cewa Sanata Shehu Sani (APC Kaduna ta tsakiya) yace jam’iyyar APC na iya rasa jihar Kaduna a zaben gwamnoni na 2019 idan gwamnatin jihar ta ci gaba da tsarin ta na cin zarafin mutane.

Sani ya yi magana ga manema labarai a Kaduna jim kadan bayan ya karbi wani korafi daga ‘yan kasuwa game da shirin Gwamna Nasir El-Rufai na rushe bababn kasuwar Barci a jihar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel