Shirin yiwa Sanata Dino Melaye kiranye: Hukumar INEC ta dan ja baya kadan

Shirin yiwa Sanata Dino Melaye kiranye: Hukumar INEC ta dan ja baya kadan

- INEC ta ja baya kan kirayen Dino Melaye

- Hukumar zabe tace ta samu umurnin kotu

- Dino Melaye dai ya ruga kotu a kwanan baya

Yanzu haka dai rayukan mutane da dama daga jihar Kogi dake a arewa ta tsakiyar Najeriya suna can a bace saboda matsayar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC a takaice ke shirin dauka kan batun kiranye da za'ayi wa Sanata Dino Melaye.

A jiya ne dai daraktan yada labarai na hukumar INEC din ya bayyana cewa hukumar zata dan ja baya kadan daga shirin yiwa Dino Melaye kiranyen har zuwa lokacin da zata kammala nazarin umurnin kotun da aka bayar kafin daga bisani ta ci gaba da shirin yin kiranyen.

Shirin yiwa Sanata Dino Melaye kiranye: Hukumar INEC ta dan ja baya kadan

Shirin yiwa Sanata Dino Melaye kiranye: Hukumar INEC ta dan ja baya kadan

NAIJ.com ta samu labarin cewa daraktan hukumar ya shaidawa manema labarai cewa a jiya sun samu takarda daga wata babbar kotu dake Abuja dangane da batun yin kiranyen.

A takardar dai hukumar ta ce kotu ta dakatar da su ne daga aikin nasu da suka fara na yin kiranyen sannan kuma ta kafa masu wasu sharuda.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel