An kama mai rawani da abokansa 6 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade a Arewa

An kama mai rawani da abokansa 6 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade a Arewa

- Assha! Mai rawani ya shiga hannu

- Mai unguwa ne dai da abokan sa 6 suka yi wa yarin ya fyade

- An gano yarinyar na da ciki wata 7

Wani bakin labari mai bakanta rai da yake iso mana yana cewa ne jami'an rundunar yan sandan Najeriya daka shiyyar Kano ta bayyana wa manema labarai cewa ta samu nasarar cafke wani mai unguwar wani kauye a karamar hukumar Dawakin Kudu da abokan sa 6 bisa laifin fyade.

Yan sanda dai sun bayyana cewa wadda akayiwa fyaden shekarunta kwata-kwata basu wuce 13 ba kuma yanzu haka likitoci sun tabbatar da cewa yarinyar na dauke da ciki wata bakwai sanadiyyar hakan.

An kama mai rawani da abokansa 6 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade a Arewa

An kama mai rawani da abokansa 6 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade a Arewa

NAIJ.com dai har ilayau ta tsinkayi jami'in hulda da jama'a na rundunar yana cewa yanzu haka dai dab suke da su kammala binciken su duka sannan kuma su maka wadanda suke zargin aikata danyen aikin a gaban kuliya.

Laifin fyade dai na neman ya zama tamkar ruwan dare a yankin arewacin kasar nan a yan shekarun nan na baya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel