Bankin duniya yace bai ci kudin Najeriya da Abacha ya kai masa ba

Bankin duniya yace bai ci kudin Najeriya da Abacha ya kai masa ba

- An zargi Janar Abacha marigayi da iyalansa da wawure kudaden Najeriya

- Mafi yawan kudaden a dala aka kwashe su

- Obasanjo yayi kokari ya dawo da wasu gida Najeriya daga kasashen waje

A cewar babban bankin duniya dai, basu san yadda aka kashe kudaden da Janar Sani Abacha ya tara ba, kuma basu kashe kudaden da hannunsu ba, wannan na zuwa ne dai a lokacin da ake bin kadin yawan kudin da Najeriya ta amso daga cikin irin kudaden, da kuma duba me aka yi da su.

Bankin duniya yace bai ci kudin Najeriya da Abacha ya kai masa ba

Bankin duniya yace bai ci kudin Najeriya da Abacha ya kai masa ba

'Kudaden dai an dawo dasu ne daga kasar Switzerland inda marigayin ya jibge su, muna bin kadin nawa aka dawo dasu, kuma ta yaya aka kashe su,' a cewar babban bankin na duniya'

A mulkin shugaba Obasanjo dai an shiga yarjejeniya domin a dawo da dukkan kudaden, amma saboda yawan su, har zuwa bana ana karbo kudaden daki daki, wadanda biliyoyi ne na daloli.

DUBA: FAdar shugaban kasa tace Buhari ne zai lashe zabukan 2019

Bankin Duniya yace muna zuba ido muga inda kudaden ke iya taimaka wa talakan Najeriya, kuma a yanzu shirin NEEDS na gwamnati ya karbi wasu kaso na kudin, wanda amfanin shirin ga talakka shine rage radadin talauci.

Babban Bankin dai ya ce suna iya kokarinsu na ganin a yanzu gwamnati ta yaki rashawa, kuma an dena kwasar kudaden kasar ana boye su a wasu kasashe.

Wannan shine dalili da yasa wasu 'yan siyasar ke tsoron kai kudaden satar su waje a wannan marra, inda suka koma boye kudaden a gidajen su da makabartu, duk dai don su arzurta kansu su su kadai da iyalansu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel