Albashin N54,000: Hakurin mu ya zo makura kan batun karin albashi - Kungiyar kwadago ta NLC

Albashin N54,000: Hakurin mu ya zo makura kan batun karin albashi - Kungiyar kwadago ta NLC

- A lokacin zabe, jam'iyyar APC tasha alwashin share wa ma'aikata kukansu

- A yanzu dai dubu 18, ne mafi kankantar Albashi

- Kungiyar kwadago na son a kai shi zuwa naira 56,000

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa, Aliyu Wabba, a tattaunawa da aka yi da shi, yayi magana akan karin albashin ma’aikata zuwa N56,00 da Gwmanatin APC ta dau alwashi kafin ta hau mulki.

Ma'aikata a Jahohi daban-daban suna kuka da rashin biyan albashi da Gwamnatin Jaha take musu. Musamman a wannan lokaci da tattalin arzikin mu yayi koma baya, ma’aikata da ‘yan fensho sune suke fuskantar kalubale wajen samun albashin su.

Hakurin mu ya zo makura kan batun karin albashi - Kungiyar kwadago ta NLC

Hakurin mu ya zo makura kan batun karin albashi - Kungiyar kwadago ta NLC

Dole shugabbaninmu da Gwamnonin Jahohi su maida biyan ma’aikata da ‘yan fensho albashinsu mafi fifiko. Suna daukan biyan albashi mara muhimmanci, amma wasu garuruwan biyan albashi yana daga cikin abin da Gwamnati ta saka a farko.

Gwamnatin tarayya tana sakin kudin biyan ma'aikata da ‘yan fensho basussukan albashinsu. Amma da zarar kudaden sun iso hannun Gwamnatin Jaha sai a neme su a rasa, su maida kudin na anfaninsu na daban.

Kungiyar Kwadago ta tsaya don ganin kudin da Gwamnatin Tarayya take saki ya iso hannun ma’aikata, ba ya makale daga sama ba. Sannan duk kudaden da gwamnatin Tarayya ta bawa Gwamnatin Jaha dole ta fadi inda suka shige da yadda aka sarrafa su.

KU KARANTA: Buhari ne zai lashe zabe a 2019, inji adar shugaban kasa

Ma’aikata da yawa suna bin Gwamnatin Jahohin su albashi. Musamman na Jahar Kogi, akwai bashin wata 15 da ba a biya albashi ba. Gwamnatin ta fake da tantance ma’aikata da take yi don ta cire ma’aikatan da basa zuwa aiki amma kafatanin su suna zuwa aiki. Benue ma tana cikin Jahohin da ma’aikata da ‘yan fensho ke bin su albashi. Haka a Jahar Oyo da Bayelsa, ma’aikata da malaman makaranta suna kuka da rashin biyan su albashi da Gwamnati bata yi.

Akwai kuma inda Gwamnati ke kokartawa kamar a Jigawa, ma’aikata basu da matsala da albashinsu. Da zarar wata ya cika ma’aikata ke samun albashinsu, 'yan fensho ma suna samun kudinsu lokacin da ma'aikaci yayi ritaya.

Hakurin ma'aikatan Najeriya ya kai bango, dole shugabbani su duba wannnan lamari. Ya kamata ace Gwamnatin Jaha ta san abin da yake muhimmi, musamman wajen biyan albashi. Tun da har akwai Jahohin da ma’aikata suke samun albashin su a dai-dai lokacin da ya kamata. To ko lallai biyan albashi ya kamata ya zamo na farko wa Gwamnati.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel