Shehu Sani ya sake karin haske kan kurayen da suka zagaye Buhari

Shehu Sani ya sake karin haske kan kurayen da suka zagaye Buhari

- Shehu Sani yace masu son Buhari kalilan ne a manyan Najeriya

- Tun rashin lafiyar Buhari, 'kuraye da dila' sun kasa zaune sun kasa tsaye

- Yace Buhari shine gatan talakka

Shehu Sani Sanata ne mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, kuma dan rajin kare hakkin dan-Adam, wanda ya sha dauri a hannun tsohon shugaban mulkin soji Janar Abacha, a yanzu kuma yake sa'insa da gwamnansa Malam Nasir El-Rufa'i.

Shehu Sani ya sake karin haske kan kurayen da suka zagaye Buhari

Shehu Sani ya sake karin haske kan kurayen da suka zagaye Buhari

A makon nan ne dai ya kira wasu 'yan siyasa da cewa su kamar kuraye ne da dilaye masu jira giwa ta fadi su sha romo.

Zargin da yayi cewa rashin lafiyar Buhari ta kara saka wasu 'yan siyasa burin kujerar tasa, kuma ma sun daina kare shugaban a fagen siyasa ta Najeriya, inda suka yi gum da bakinsu, sai dai jiran ko ta kwana.

KU KARANTA: Buhari ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2019

Sanata Shehu Sani ya ce Buhari ne gatan talakan Najeriya, inda ya kara da cewa ba zagi bane idan ya kira talakka da karamar dabba wadda zaki Buhari ke karewa daga miyagun dabbobi.

A hirarsa a yau da safen nan da sashen Hausa na BBC, Sanata Shehu Sani ya ce manyan 'yan siyasar kasar nan sun kasa zaune sun kasa tsaye tun ganin su shugaba Buhari ya koma asibiti, inda yace suna ta kulle-kulle da makirce-makirce.

Ya kuma yaba da A'isha Buhari a matsayin jarumar mace wadda ta mara wa hasashensa baya, kan cewa Addu'ar talakawa ta karbu, Buhari zai dawo ya karbi iko na mulkin da ya faro.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel