Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Naira triliyan 2.7 don biyan fanso da albashin ma'aikata

Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Naira triliyan 2.7 don biyan fanso da albashin ma'aikata

- Gwamnatin tarayya zata biya basussukan da ma'aikata ke binta

- Gwamnatin ta amince da N2.7 tiriliyan don yi hakan

- Basussukan tun daga 1994 za'a biya

Majalisar zartarwar Najeriya dake yin zamanta na sati-sati ta amince da zunzurutun kudin da suka kai tsabar Naira triliyan 2.7 domin biyan ma'aikan ta basussukan da suke bin ta.

Babbar ministar kudi Misis Kemi Adeosun ce da bayyana hakan ga maneman labarai a jiya a fadar shugaban kasar dake a garin Abuja babban birnin tarayya jim kadan bayan gama taron nasu na sati-sati.

Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Naira triliyan 2.7 don biyan fanso da albashin ma'aikata

Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Naira triliyan 2.7 don biyan fanso da albashin ma'aikata

NAIJ.com ta samu labarin cewa tsabar kudin za'a biya albashi ne da kuma fansho da dai sauran wasu basussukan da ma'aikatan gwamnatin tarayyar ke bin gwamnatin tun daga shekara ta 1994.

Kafin nan dai mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya kai wa shugaba Buhari ziyara a kasar Birtaniya inda yake jinya kafin ya dawo ya jagoranci taron.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel